Bankuna Sun Kira Kwastomomi Su Su Zo Karbi Sabbin Kudi, Amma Sun Rage Lokacin Tashi
- Bankunan Najeriya sun nemi kwastomominsu da su zo cire wani adadi na kuri a kan kanta a fadin kasar a halin da ake ciki
- Bankunan sun ce, za su ba kwastomomi kudin ne ta hanyar bin ka’idar wanda ya fara zuwa a fara bashi kamar yadda rahoto ya fada
- A boye, bankunan Najeriya sun rage lokacin rufewa, watakila saboda zaben shugaban kasa da aka yi a kwanakin baya
Wasu bankunan Najeriya sun kira kwastomominsu da su zo don cire kudin da bai taka kara ya karya ba duk da halin da ake ciki.
Bankuna da yawan da suka bude a ranar Talata, 28 ga watan Faburairu, sun ce suna da kudi a wurin ajiyarsu, amma adadi ne mara yawan da zai wadaci bukatar kowane kwastoma.
A cewar bankunan, za su ba da kudi ga duk wanda ya fara zuwa kasancewar kudaden da suke dasu basu da yawa.
An sake ci gaba da layi a bankunan Najeriya
A bangare guda, dogon layi ya dawo a bakin bankunan kasar nan a ranar 28 ga watan Faburairu, inda aka ga mutane da yawa suke neman yadda za su cire kudin.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Legit.ng ta tattaro cewa, da yawan bankuna basu bude ba, wadanda suka bude kuwa ba a cika barin kwastomomi su shiga don cire kudin ba.
Wani ma’aikacin bankin Eco a jihar Legas ya shaidawa wakilinmu cewa, an umarci bankin da ya rufe da wuri a ranar.
Ya ce:
“Jiya (Litinin 27 ga watan Faburairu 2023), mun rufe da misalin 3 na yamma a yau kuma (Talata), sun ce sun mu rufe da wuri.
A cewarsa, ma’aikatan bankin da kansu suna cikin wani yanayin rudu a wannan lokacin kuma sukan hana kwastomomi shiga banki.
“Mun tura sako ga wasu kwastomomi don fada musu sabon tsaron da kuma sabon lokacin rufewa."
Wani ma'aikacin bankin Jaiz a jihar Gombe ya shaidawa wakilinmu cewa, har yanzu akwai karancin kudi a bankunan, shi yasa ba sa samun ba kwastomomi kudin da yawa.
A cewarsa:
"Kudin ne babu da yawa, mutane kuma sun damu sai an ba su a madadin su koyi amfani da wasau hanyoyi daban-daban na musayar kudi."
‘Yan Najeriya na ci gaba da fafutukar neman tsabar kudi
Zaben shugaban kasa da aka yi a Najeriya ya batr ‘yan kasar cikin halin kunci kasancewar tattalin arzikin kasar ya sauya.
‘Yan Najeriya na shan fama wajen neman sabbin N200, N500 da N1000 tun bayan da CBN ya sanya wa’adin daina amfani da tsoffin kudi a ranar 10 ga watan Faburairu.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya sa baki aka bar tsoffin N200 da su ci gaba da yawo a kasar har zuwa ranar 10 ga watan Afrilun 2023.
Har yanzu dai tsoffin N200 ba a cika samunsu a bankunan Najeriya ba duk da umarnin Buhari.
Asali: Legit.ng