Bayan Umurnin Buhari, Har Yanzu Ko N200 Ba'a Samu a Bankuna

Bayan Umurnin Buhari, Har Yanzu Ko N200 Ba'a Samu a Bankuna

  • Yan Najeriya sun koka kan rashin tsabar kudi har yanzu, kimanin makonni uku da shiga wannan hali
  • Har yanzu kwastamomi sun bayyana cewa basu samu tsaffin N200 da Buhari yace a fitar ba
  • Saura mako guda zabe, gwamnoni goma sun kuma maka Buhari a kotu kan wannan lamari na kudi

Abuja - Wasu kwastamomin bankuna a birnin tarayya Abuja sun koka kan rashin samun kudi ko da tsaffin N200 duk da umurnin Shugaba Muhammadu Buhari.

Legit Hausa ta kawo muku rahoto ranar Alhamis inda Shugaba Muhammadu Buhari ya umurci bankin CBN ya fito da tsaffin N200 saboda halin da mutane suka shiga sakamakon sauya fasalin kudi.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya ruwaito cewa dukkan bankunan da aka ziyarta har yanzu basu fara bada tsaffin N200 ba.

Kara karanta wannan

Na Kadu Da Jin Yadda Gwamnonin APC Ke Caccakar Buhari Kan Sauya Kudi, Kwankwaso

Effyi
Bayan Umurnin Buhari, Har Yanzu Ko N200 Ba'a Samu a Bankuna
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wasu kwastamomi da suka tattauna da NAN ranar Lahadi a Abuja sun bayyana cewa bankuna suna yiwa wanna kasasr zagon kasa.

Mr Tunde Ade, wani kwastama ya yi kira ga bankuna su tashi tsaye suyi ayyukansu yadda ya kamata.

Yace:

"Na shiga banki a Central Area don samun kudi wa iyali ne yayinda karshen mako ya gabato, amma na'urar ATM bata aiki kuma babu kudi cikin bankunan."
"Sauran kwastamomin da ke wajen sun ce ma'aikatan bankunan da jami'an tsaronsu sun kulle bankin kuma sun hana mutane shiga."
"Wannan ba shi da kyau. Alal akalli ya kamata su saki tsaffin N200 ga kwastamomi kamar yadda shugaban kasa yayi umurni."

Wani kwastoman daba, Sanni Abbas, ya caccaki bankuna.

Yace:

"Bankunan ba su da tausayi. Menene ya hanasu budewa yau, kuma su zuba kudi cikin ATM dinsu"

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Yi Halinta: An Gano Mutum 2 Da Suka Sauya Wa Buhari Tunani Kan Tawaita Wa'adin N500 da N100

Wani kwastoman, Muhammad Sule, ya yi kira ga bankunan su tausayawa yan Najeriya bisa wahalhalun da suke ciki.

Yace:
"A lokaci irin wannan, ya kamata bankuna su fahimci cewa akwai hakkin ragewa yan Najeriya wahalar da suke ciki."
"Da CBN na fitar da isassun sabbin kudi da tsaffin N200, da matsalar tayi sauki."

Jerin Gwamnoni 10 Sun Sake Maka Buhari Kotu, Sun Bukaci A Soke Umurninsa Kan N200

Jihohi goma sun bukaci kotun koli ta soke umurnin Shugaba Muhammadu Buhari kan dawo da tsaffin N200 kadai ba tare da N500 da N1000.

Sun sanar da kotun cewa wannan ya sabawa kundin tsarin mulkin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel