Karancin Naira: Wata Mata Yar Najeriya Ta Biya Mai Gyaran Takalmi Da Abinci Bayan Ya Yi Mata Gyara

Karancin Naira: Wata Mata Yar Najeriya Ta Biya Mai Gyaran Takalmi Da Abinci Bayan Ya Yi Mata Gyara

  • Wata mata da ke amfani da shafin Twitter ta bada labari mai taba zuciya kan wahalar da talakawa ke ciki
  • Matar ta kira mai gyaran takalmi ya yi mata aiki, kuma ya koka kan cewa bai samu abinci ba bayan tafiya a kafa na awa uku
  • Matar mai tausayi ta ce labarinsa ya taba zuciyarta, hakan yasa ta bashi shinkafa ya ci sannan ta

Duk da fatan da ake yi na samun nasarori a gaba, sabon tsarin rage yawan kudin takarda da babban bankin kasa, CBN, ta ke aiwatarwa ya taho da wasu yan wahalhalu da al'umma ke fuskanta.

Wani bidiyo da ya fito a baya-bayan nan ya nuna irin wahalar da talakawa a Najeriya ke sha saboda wannan sabon tsarin na kayyade kashe tsabar kudi.

Kara karanta wannan

“Ka Karya Mun Zuciya”: Matashi Ya Saka Yagaggun Kaya Masu Datti, Yana Nunawa Mace Mai Tabin Hankali So, Bidiyon Ya Yadu

Budurwa da mai gyaran takalmi
Wata mata ta ba wa mai gyaran takalmi shinkafa bayan ya koka kan rashin kudi. Hoto: Photo Credit: Tim Robberts, Christopher Furlong, Anadolu agency
Asali: Twitter

Wata mai amfani da shafin Twitter mai suna @HelenTemitope ta wallafa abin da ya ci karo da shi.

Tana kokarin gyara takalminta ne sai mai gyaran takalmin ya fada mata ta kawo masa kudi, ko tsoho ko sabo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya fada mata cewa ya yi tafiya a kasa na fiye da awa uku kuma bai samu kwastoma ba sannan bai ci abinci ba.

Matar, mai kirki ta yanke shawarar ba shi abinci sannan ta bashi garin rogo, bayan ya kammala aikin da ta bashi.

Ta kuma yi amfani da wannan damar don tuna wa al'umma cewa mutane da dama na shan wahala sakamakon wannan sabon tsarin.

Ta ce:

"Kafin yau, ban taba sanin munin halin da wannan rashin takardan nairan ya jefa al'umma ba. Na kira mai gyaran takalmi ya yi min aiki. Ya ce in kowa ko wane kudi da na ke da shi domin ba shi da kudi kuma bai ci abinci ba a ranar, ya yi tafiya na fiye da awa uku, na tausaya halin da ya shiga."

Kara karanta wannan

Baiwa Daga Allah: Bidiyon Uwa Mai Hannu Daya Tana Rangadawa Diyarta Kitso Ya Yadu

Martanin masu amfani da dandalin sada zumunta

@rosie_martinee ta ce:

"Ya kamata a dauki matakan tabbatar cewa an aiwatar da wannan tsarin cikin sauki amma ba haka Buhari ya saba yi ba. An soke ganawar da zan yi karfe uku saboda karancin naira."

Setemi @Setemi ya rubuta:

"Kuma sai kin garzaya kin taho nan kin fada mana abin da kika ba shi ko? Da kawai kin ce mutane suna shan wahala."

@Officialshyne 18:

"Ina mamakin yadda mutanen da kullum sai sun fita su nemi na abinci suke rayuwa, wannan abin ya munana."

@AgboolaAlaka ya rubuta:

"Ina zaton wasu sun ce wannan tsarin an yi shi ne don wahal da yan siyasa, yanzu wa ke wahala? Yanzu na karba mabudin dakin ajiye kaya daga wani ma'aikaci wanda ya ce bai san inda zai samu kudin zuwa wurin aiki gobe ba. Obidients na tunanin wannan tsarin zai taimaka wa PO."

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari Ya Zolaye Ganduje: Ka Tafi Ka Kai Tsaffin Nairan Ka CBN Idan Na Halas Ne

@DarkHorseSteve ya ce:

"Allah ya miki albarka. Ba ki san irin abin da ki ka yi wa mutumin nan ba. Ina mamakin yadda mutane ke rayuwa saboda wannan tsarin a yanzu."

A wani rahoton kun ji cewa yan kasuwa sun yi fatali da umurnin babban bankin Najeriya, CBN, suna cigaba da karbar tsaffin kudi a Legas.

Cigaba da hada-hada da tsaffin kudin ya saba umurnin babban bankin kasa amma ya ci karo da umurnin kotun koli na kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel