Matashiya Mai Hannu Daya Ta Tsantsarawa Diyarta Kitso a Bidiyo

Matashiya Mai Hannu Daya Ta Tsantsarawa Diyarta Kitso a Bidiyo

  • Wata uwa mai hannu daya ta tsantsarawa diyarta kitso an kuma dauki bidiyon yadda lamarin ya wakana
  • An wallafa bidiyon ne a TikTok kuma ya nuna yadda uwar ta dungi ba diyar tata kulawa cike kauna
  • Matar ta raba gashin kan yarinyar gida-gida sannan ta kitsa shi a wani bidiyo da ya ba mutane 27.3k mamaki

Wani hadadden bidiyon iyali ya nuna lokacin da wata uwa wacce ke dauke da hannu daya take kitsawa diyarta gashin kanta.

A wani bidiyo da ya yadu a TikTok wanda shafin @velyndaresetanatu ya wallafa, an gano cewa uwar hannu daya ne da ita.

Uwa da diyarta
Matashiya Mai Hannu Daya Ta Tsantarawa Diyarta Kitso a Bidiyo Hoto: @velyndaresetanatu.
Asali: TikTok

Yayin da hannunta na hagu ke nan lafiya kalau, an yanke hannunta da dama tun daga gwiwar hannu har kasa.

Mata mai hannu daya tana kitsa kan diyarta

Kara karanta wannan

An Gano Wata Kyakkyawar Tsohuwa Mai Shekaru 150 a Najeriya, Bidiyonta Ya Ba Da Mamaki

Sai dai kuma nakasar da take da shi bai hana ta kula da diyar tata da gyara mata gashin kanta ba cike da so da kauna.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ta yi amfani hannunta mai lafiya wajen raba gashin gida-gida kafin ta fara kitsa shi. Yanayin yadda take kitsa kan da kyau shine ya dauka hankalin jama'a kuma ya sanya bidiyon yaduwa.

A halin yanzu, bidiyon ya yadu a TikTok ya kuma samu fiye da mutum 574 da suka kalla da likes fiye da 27.3k.

Kalli bidiyon a kasa:

Yadda makauniya ta ke rangada kitso da daurin dankwali ya bar mutane baki bude

A wani labarin, mun ji cewa wata matashiya mai lalurar makanta ta yi suna a duniyar yanar gizo saboda wani baiwa na musamman da Allah ya yi mata na iya kitso da daurin dankwali.

Kara karanta wannan

Sabon salo: Bidiyon yadda wani ya tsiro da hanyar yin aski da cokali, jama'a sun kadu

A wani bidiyo da ya yadu a wanda shafin a wani bidiyo da Michael Thompson Showunmi ya wallafa a Twitter, an gano yarinyar mai suna Victoria tana bayyana fasaha da baiwa.

Duk da kasancewarta makauniya, Victoria na yi wa abokan karatunta kitso cikin kwarewa.

An dai gano ta cike da kwarewa ta kama gashin wata daliba da mataji gami da kitsawa tamkar wata mai gani da idonta.

Bayan kitso, matashiyar ta kuma iya daura dankwali irin na amare wato gwaggwaro kuma ta ce yanzu abun da ya rage mata shine koyon kwalliya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel