Kai Tsaye: Yadda Shari’ar Gwamnoni v FG a Kan Canjin Kudi Ke Gudana a Kotun Koli

Kai Tsaye: Yadda Shari’ar Gwamnoni v FG a Kan Canjin Kudi Ke Gudana a Kotun Koli

A yau 22 ga watan Faburairun 2022 ne za a ci gaba da zaman kotun koli a karar da wasu gwamnonin Najeriya suka shigar kan gwamnatin tarayya, musamman Babban Banakin Najeriya (CBN).

Karar da gwamnonin suka shigar ba komai bane manufarta illa ganin an tsawaita wa'adin daina amfani da tsoffin kudade.

A makon da ya gabata, mun kawo muku yadda aka kaya a zaman kotun, inda aka dage ci gaba da zaman zuwa yau Laraba.

A yau, za mu ci gaba da kawo muku yadda ake ci gaba da zaman a kotun don ji yadda za ta kaya.

An dage kara zuwa 3 ga watan Maris

Bayan sauraran batutuwa daga lauyoyi da masu ruwa tsaki, an dage ci gaba da sauraran karar zuwa 3 ga watan Maris din bana.

Karshen zaman da aka yi a kotun kenan a yau Laraba 22 ga watan Faburairun 2023.

Jihohin Edo da Bayelsa

Audu Anuga SAN wanda ya tsayawa jihar Bayelsa yana goyon bayan Agabi SAN. Haka lamarin yake ga Lauyan Edo, Kenneth Mozea SAN.

Mai shari'a Inyang Okoro yana ta kokawa a kan yadda aiki ya yi wa kotun koli yawa.

Martanin Lauyan Gwamnati

Kanu Agabi SAN mai kare gwamnatin tarayya ya bukaci kotu tayi watsi da karar, ya soki yadda ba a cusa bankin CBN a cikin wannan shari'ar ba.

Lauyan ya ce tun kafin 16 ga watan Fubrairu, mutane sun daina karbar tsofaffin kudi, ya ce shugaban kasa ya dauki mataki ne saboda ya ceci kasa.

An shigo da Kuros Riba, Ogun, Ekiti

Jihar Kuros Riba ta bi sahun sauran Gwamnonin da suka shigar da kara yayin da Tunde Afe -Babalola SAN yake kare gwamnatin jihar Ogun a shari’ar.

Barista O. O. Olowolafe SAN shi ne lauyan da ya tsayawa gwamnatin jihar Ekiti a kotun kolin.

Kwamishinan shari'a na jihar Ondo, Sir Charles Titiloye, SAN ya shiga cikin masu tuhuma, rokonsa ya zo daya da na jihohin Zamfara, Kaduna da Kogi.

Daily Trust ta rahoto babban lauyan gwamnatin Abia kuma Kwamishinan shari’ar jihar, Udochi Iheanacho Esq ya bukaci ya shiga cikin masu yin kara.

Gwamnatin Legas ta dauki zafi

Kwamishinan shari’a na jihar Legas, Moyosore Onigbanjo SAN yana so a ki sauraron gwamnatin tarayya har sai sun yi biyayya ga umarnin babban kotun Najeriya.

Matsayar Zamfara da sauran Jihohi

Lauyan jihar Zamfara, J. Owonikoko, SAN ya roki Alkalai su soke umarnin da shugaba Muhammadu Buhari ya bada bayan kotu ta zauna.

Owonikoko, SAN yana so kotun koli ta bada damar a cigaba da amfani da tsofaffin N500 da N1000.

M. A Ologunorisha a matsayinsa na Lauyan Gwamnatin jihar Katsina yana tare da Kaduna, Kogi da Zamfara.

Tsohon Gwamna yana kare Kaduna

Aruleba ya ce M.A. Abubakar SAN shi ne yake jagorantar Lauyoyin da suka shigar da kara a gaban babban kotun kasar a madadin jihar Kaduna.

Sauran lauyoyin da suka tsayawa Gwamnatin Kaduna sun hada da A. B. Sulu- Gambari da Shuaib Ahuwa, SAN . Za a saurari shari'arsu.

Za a fara da shari'ar Jihar Kaduna

Bayanan da muka samu daga Facebook sun tabbatar da cewa kotun kolin zai fara da sauraron shari'ar Jihar Kaduna da gwamnatin tarayya.

An cigaba da zama

Bayan an mike kafafu, kotu zai cigaba da sauraron shari'ar da ake yi a kan canza kudi da gwamnan bankin CBN ya yi da amincewa gwamnati.

Alkalan kotun koli sun amince jihar Abia ta shiga sahun wadanda suke karar gwamnati.

An tafi gajeren hutu

Gbenga Aruleba wanda yana halartar zaman kotun ya ce Inyang Okoro ya bada hutun mintuna goma domin a huta kafin a cigaba da shari’ar a garin Abuja.

Kafin nan, Alkalin mai jagorantar zaman ya koka da cewa ana neman amfani da kotu wajen samun wanda za a zarga a sabanin gwamnatin tarayyan da jihohin.

Jihohi 2 na tare da Gwamnatin tarayya

Majiyarmu ta tabbatar da cewa Jihohin Edo da na Bayelsa su na tare da Lauyan gwamnatin tarayya kuma Ministan shari’a na kasa, ba su goyon bayan takwarorinsu.

Idan ba a manta ba, tsohon Ministan shari’a, Kanu Agabi, SAN shi ne shugaban lauyoyin da suka tsayawa gwamnatin tarayya a wannan kara da ake yi a kotun koli.

Dole ne mu yanke hukunci a yau, Kotun Koli ya yi magana kan karar gwamnoni da FG

Kotun koli ta bayyana cewa, a yau ne zai tabbatar da yanke hukunci game da karar dokar musayar kudi ta CBN.

Gamayyar alkalai bakwai na kotun kolin karkashin jagorancin mai shari'a Inyang sun ce kotun ba za ata sake barin wata jiha ko tsagi ya sake shiga cikin karar ba kamar yadda suka bari a makon jiya.

Yau za a zartar da hukunci

Mai shari'a Amina Augie ta tabbatar da cewa a yau za a yanke hukunci a wannan shari'a. Alkalin ta nuna ba za a daga karar ba.

Maiyarmu ta tabbatar da cewa kotun koli za ta saurari karar daki-daki da safiyar nan.

Bukatar Lauyoyin Ribas

Emmanuel Ukala da wasu manyan Lauyoyi uku da suka tsayawa jihar Ribas sun bukaci shiga cikin masu gabatar da kara.

Daya daga cikin Lauyoyin Gwamnati, T.A Gazali bai yi adawa da wannan roko ba. Alkalai za su yanke hukunci a kan lamarin.

Jihar Ribas ta shiga cikin masu kara

Bayan kusan minti 15 da fara sauraron shari'ar sai Alkali Inyang Okoro ya amince da bukatar Gwamnatin Ribas na shiga cikin masu tuhumar gwamnati.

Duka sauran Alkalan da ke zaman shari'ar sun amince da wannan bukata.

Kotu ta fara zama

Kamar yadda Gbenga Aruleba wanda ma'aikacn gidan rediyo ne ya kawo rahoto, da kimanin karfe 9:05 na safe kowa ya zauna, kotu ta fara sauraron shari'ar.

Alkalai bakwai suke sauraron wannan kara a karkashin jagorancin Mai shari'a Inyang Okoro.

Online view pixel