CBN Ya Musanta Jita-Jitar Kara Wa'adin Amfanin Tsoffin N500 da N1000

CBN Ya Musanta Jita-Jitar Kara Wa'adin Amfanin Tsoffin N500 da N1000

  • CBN ya musanta rahoton da uwar gidan shugaban kasa, Aisha Muhammadu Buhari, ta wallafa a shafukanta na soshiyal midiya
  • Aisha Buhari ta wallafa takarda da safiyar nan cewa babban bankin ya tsawaita wa'adin amfanin da tsoffin naira
  • A wata sanarwa da Daraktan sashin sadarwa na CBN ya fitar, ya ce labarin ba gaskiya bane

Abuja - Babban bankin Najeriya (CBN) ya musanta wata takarda da Aisha Buhari, uwar gidan shugaban ƙasa ta wallafa a shafinta cewa ya tsawaita wa'adin amfani da tsoffin kuɗi.

A wata sanarwa da CBN ya fitar a shafinsa na Tuwita, ya yi kira ga ɗaukacin 'yan Najeriya da su yi fatali da kowane saƙo ko bayanan ƙarya waɗanda ba daga bankin suka fito ba.

Aisha Buhari.
CBN Ya Musanta Jita-Jitar Kara Wa'adin Amfanin Tsoffin N500 da N1000 Hoto: CBN
Asali: Facebook

Uwar gidan shugaban kasan ta wallafa cewa CBN ya amince da ƙara wa'adin ci gaba da amfani da tsoffin takardun N200, N500 da N1000 har zuwa ranar 1 ga watan Mayu, 2023.

Kara karanta wannan

Waraka Ta Samu: CBN Ya Ɗauki Sabbin Matakai Masu Kyau, Ya Sake Fito da Tsoffin Naira N200

Menene gaskiyar labarin?

Sai dai a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Daraktan sashin yaɗa labarai, Osita Nwanisobi, CBN ya musanta rahoton da cewa ba gaskiya bane.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sanarwan ta ce:

"An ja hankalin CBN game da wani labarin karya mara asali da ke yawo wanda ya yi ikirarin babban banki ya umarci bankunan kasuwanci su ci gaba da karɓan tsohon N500 da N1000."
"Domin fayyace gaskiya duba da jawabin da shugaban ƙasa ya yi kai tsaye ranar 16 ga watan Fabrairu, CBN ya umarci bankuna su baiwa mutane tsoffin N200 kaɗai har zuwa 10 ga watan Afrilu, 2023."
"Saboda haka muna kira ga ɗaukacin 'yan Najeriya su yi watsi da duk wani labari wanda ba daga babban bankin kasa ya fito a hukumance ba game da wannan batun."

Daga karshe, CBN ya shawarci kafafen watsa labarai su rinka tace labaransu daga sahihan majiya kafin su wallafa.

Kara karanta wannan

Magana Ta Kare: EFCC Ta Yi Magana Kan Raɗe-Raɗin Ta Kai Samame Gidan Tinubu, Ta Gano Sabbin Kudi N400bn

A wani labarin kun ji cewa CBN ya bar Fotal ɗin cike Fam domin maida tsaffin takardun naira zuwa bankuna a Buɗe

Bayanai sun nuna cewa ganin haka ya sa kwastomomi suka ci gaba da zuwa bankuna suna ajiye kuɗi, sun yaba da yadda aka saurare su har a ranakun hutun karshen mako.

Asali: Legit.ng

Online view pixel