Mutane Sun Ci Gaba da Kai Tsohon Naira Bankuna Yayin da CBN Ya Bar Shafi a Bude

Mutane Sun Ci Gaba da Kai Tsohon Naira Bankuna Yayin da CBN Ya Bar Shafi a Bude

  • Kwastomomin bankuna sun ci gaba da maida kuɗinsu cikin daɗin rai yayin da CBN ya bar shafin maida kuɗin a bude
  • Har ranakun karshen makon nan Fotal ɗin CBN na nan a bude kuma mutane sun yaba da yadda bankuna suke sauraronsu
  • Sai dai akwai wadanda ke fuskantar matsaloli yayin maida tsoffin kuɗinsu duk da sun bi matakan da aka gindaya

'Yan Najeriya sun ci gaba da tururuwar zuwa bankunan kasuwanci domin maida tsoffin takardun N500 da N1000 a ranar Litinin 20 ga watan Fabrairu, 2023.

Leadership tace lamarin ya zo da sauki yayin da babban bankin Najeriya ya bar shafin yanar gizo na cike Fam ɗin maida tsoffin kuɗin a buɗe.

Tsoffin naira.
Mutane Sun Ci Gaba da Kai Tsohon Naira Bankuna Yayin da CBN Ya Bar Shafi a Bude Hoto: CBN
Asali: Depositphotos

Har zuwa daren ranar Litinin shafin a buɗe yake ga kowane ɗan Najeriya mai niyyar tarkata tsoffin kuɗin da aka haramta ya maida su banki don gudun asara.

Kara karanta wannan

Tsoffin Naira: CBN Ya Karyata Labarin da Aisha Buhari Ta Wallafa a Shafukan Sada Zumunta

Kwastomomin bankuna sun nuna farin ciki da cewa wannan tsarin ya saukaƙa wahala domin mafi yawan bankuna suna saka wa mutane kuɗin nan take idan sun maida.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A ranar Laraban da ta gabata ne CBN ya bude shafin yanar gizon bayan shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya ce tsohon N500 da N1000 sun tashi aiki yayin da N200 zata ci gaba da amfani har zuwa 10 ga watan Afrilu.

Tun fari CBN ya bude Fotal ɗin maida tsoffin takardun naira har zuwa ranar Jumu'a 17 ga watan Fabrairu, 2023, abin mamakin shafin na nan bude a karshen makon nan kuma Bankuna sun fito domin sauraron masu zuwa aje kuɗi.

Wata ma'aikaciya a jihar Legas, Nike Adebayo, wacce ta zanta da jaridar ta ce wani bawan Allah ne ya taimaka mata ta cike Fam ɗin ranar Lahadi ta haɗa lambobin kai kuɗin.

Kara karanta wannan

Waraka Ta Samu: CBN Ya Ɗauki Sabbin Matakai Masu Kyau, Ya Sake Fito da Tsoffin Naira N200

Amma sakamakon Bankin ba ya aiki ranar Lahadi, ba ta samu damar maida tsoffi naira N4,500 da suka rage mata ba.

Wasu kwanstomomi sun koka kan cewa bankunansu basu saka masu kuɗin nan take. Mista Akin ya bayyana cewa ganin yadda mutane ke samun sakon shigar kuɗi asusu nan take, ya garzaya ya cike Fam.

"Na kai ajiyar kuɗina banki tun da daɗewa amma yanzu suna gayamun sai na jira CBN ya tabbatar da bayanan Asusuna sannan zasu bani kuɗin," inji shi.

Bisa haka ne Legit.ng Hausa ta tuntubi wani ma'aikacin First Bank reshen Zariya, ya ce akwai matsala sosai idan haka za'a ci gada tafiya kafin naira ta wadata a hannu.

Ya faɗa wa wakilin mu cewa suna fama da mutane masu son cire kuɗi amma su kansu basu samun isassun takardun kuɗin daga CBN.

"Har yanzu babu isassun takardun naira daga CBN, tsoffin N200 da aka ce za'a ba jama'a ba sabon bugu bane, waɗanda muka karbe ne za'a kara rabawa jama'a."

Kara karanta wannan

Talaka Na Shan Wuya, Duk Da Ina Gwamna Sababbin Kuɗin Sun Yi Min Wuyar Samu -Gwamna Ya Koka

"Sabbin kuɗin da aka sauya sun yi wahala, ba a hannun mutane ba har mu nan a banki, ga kwastomomi sun matsa mana, gaskiya dai akwai sauran aiki," inji shi.

CBN Ya Musanta Jita-Jitar Kara Wa'adin Amfanin Tsoffin N500 da N1000

A wani labarin kuma CBN ya karyata rahoton da Aisha Buhari ta wallafa a shafinfa game da tsawaita wa'adin tsoffin naira

A ɗazu da safe ne, uwar gidan shugaban ƙasan ta wallafa wata sanarwa cewa CBN ya kara tsawaita halascin tsoffin naira har zuwa 1 ga watan Mayu.

Amma daraktan sashin yaɗa labarai na CBN ya musanta rahoton da cewa ba shi da tushe ballantana makama, ya roki yan Najeriya su yi watsi da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel