Canjin Kudi Ya Jawo Karuwai Su na Kuka, Ana Samun Karancin Abokan Yin Lalata
- Wasu daga cikin matan da suke zaman kan su a garin Abuja ba su ji dadin canza takardun kudi ba
- Da aka zanta da matan sun nuna cewa ana samun kalubale wajen tura masa kudi a asusun bankinsu
- A dalilin karancin kudi a hannun jama’a, wasu kan yi rangwamen dole idan mutum na da kudi
Abuja - Mata masu zaman kan su a babban birnin tarayya Abuja, sun nuna yadda suke fama da rashin ciniki a dalilin canza manyan kudi da aka yi.
Hukumar dillacin labarai na kasa ta zanta da wasu daga cikin wadannan mata da suke zaman kan su, domin jin yadda suke neman kudi a halin yanzu.
Matan sun bayyana cewa karancin takardun kudi ya jefa kasuwancinsu a wani halin ha’ula’i, su na ganin tsarin da aka zo da shi barazana ne a gare su.
Duk da alheran da suke gani tattare da sauya kudin da aka yi, matan sun nuna abin ya taba su.
Babu kaya a kasa
Wata Miss Alexandra Tricia (an sakaya sunanta) ta fadawa manema labarai cewa abokan lalatarta sun ragu sosai saboda kowa yana kukan babu kudi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alexandra Tricia ta ciza yatsa a kan tsarin da bankin CBN ya fito da shi, ta ce abin duk takaici domin yanzu sana’ar ta su ta tsaya cak a birnin tarayyar.
"Yanzu ba a samu sosai a harkar domin a yau babu takardun kudi a ko ina. Idan an yi ciniki, wasu abokan harkar sai su tambayi lambar akawun dinka.
Sai dai su ce za su aika maka kudi ta akawun, idan na bada lambar asusun, sai su latsa wayarsu, sai su fada mani cewa ai sun aiko mani da kudina.
Abin bakin cikin shi ne zan ga kudi ya fita daga asusunsu, amma ni ba zan ji kudi sun shigo ba, kuma sai su ce nan take suke neman biyan bukatarsu.
Idan ka ki yarda ka bada hadin-kai kafin ka ji shigowar kudi, wasu sai su fara rigima.
Farashi ya yi kasa yanzu
The Guardian ta rahoto cewa dole wasu matan kan rage farashinsu idan suka samu wanda yake da kudi a hannu, a maimakon ya tura masu ta akawun.
Wata mai wannan aiki ta ce akwai matan da suka dakata daga harkar nan saboda rashin kudi da ake fama da shi tun da aka buga sabbabbin Nairori.
Innalillahi Wa inna Ilaihir Raji'un
A wani rahoto da mu ka fitar, an tabbatar da labarin rasuwar Hon. Kamilu Ado Wudil. Jami'in na NSCDC ya rasu ne saura kwanaki shida ayi zabe.
Hon. Kamilu Ado Wudil shi ne ‘Dan takaran Jam'iyyar NNPP a zaben ‘dan majalisar wakilan tarayyar Wudil/Garko a zaben da za ayi a makon nan.
Asali: Legit.ng