Dokokinku Suna Cutar da Talakawan Najeriya, Atiku Ya Caccaki CBN, Ya Fadi Shirinsa

Dokokinku Suna Cutar da Talakawan Najeriya, Atiku Ya Caccaki CBN, Ya Fadi Shirinsa

  • Dan takarar shugaban kasa a PDP ya ce ba zai bari ‘yan Najeriya su sha wahala a mulkinsa ba ko kadan
  • Ya ce duk wanda yake da kudin halali zai kai kudinsa banki idan ya gaji kujerar Buhari a zaben makon karshen mako
  • Hakazalika, ya ce shirinsa kawo ci gaba ne bai wai kuntatawa jama’a babu gaira babu dalili a irin wannan yanayin

Najeriya - Alhaji Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP ya tabbatarwa ‘yan Najeriya cewa, idan aka zabe shi ya gaji Buhari a zaben bana zai tabbatar babu wanda ya yi asarar halalinsa na kudi game da dokar CBN.

Dan takarar ya bayyana hakan ne ta shafinsa na kafar sada zumunta, inda ya bukaci Babban Bankin Najeriya (CBN) da ya bar bankunan kasuwanci su ci gaba da karbar tsoffin N500 da N1000 don ragewa ‘yan Najeriya radadi.

Kara karanta wannan

Na Kadu Da Jin Yadda Gwamnonin APC Ke Caccakar Buhari Kan Sauya Kudi, Kwankwaso

Atiku ya caccaki shirin CBN da Buhari
Dokokinku Suna Cutar da Talakawan Najeriya, Atiku Ya Caccaki CBN, Ya Fadi Shirinsa | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Hakazalika, ya bukaci CBN da ya taimaki ‘yan kasa ya tabbatar da wanzuwar sabbin kudaden da ya buga a ko ina a kasar.

Kalaman Atiku masu daukar hankali

A cewar Atiku:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Dokar CBN na cutar da talakan Najeriya da kuma wadanda suka tara kudi da guminsu. Babban bankin ya kamata, a cikin gaggawa, ya bar bankunan kasuwanci suke karbar tsoffin N500 da N1000.
“Ya kamata sabbin kudaden nan su wadata domin ragewa talakawa radadin da suke ciki.
“Ina tabbatar muku idan muka karbi mulki ta hanyar samun kuri’unku, gwamnatin PDP ba za ta bar ‘yan Najeriyan da suka samu kudi ta hanyar guminsu su yi asarar ko kobo daya ba.
“Za ku iya daukar wannan alkawarin ga banki domin manufarmu ita ce kawo ci gaba ba wai kuntatawa mutanenmu ba.”

Kada a kara wa’adin daina kashe tsoffin kudi, cewar Atiku a baya

Kara karanta wannan

2023: 'Yan Najeriya sun gaji da Buhari, matar Atiku ta yi bayanai masu daukar hankali

A baya kuma, Atiku ya ce bai kamata Babban Bankin Najeriya ya tsawaita wa’adinsa na daina amfani da tsoffin kudi ba saboda wasu dalilai.

Atiku ya bayyana cewa, matukar ana son ganin sauyi a shirin da babban bankin ya dauko, to tabbas dole ne a amince da dokar ba tare da tsawaita ta ba.

Maganar Atiku na zuwa ne daidai lokacin da wasu ‘yan siyasar nan ke sukar shirin CBN na sauya kudi da kuma tabbatar da karar da tsoffi a hannun mutane.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.