Bidiyon Yadda Wani Dan Najeriya Ke Amfani da Cokali Wajen Aski, Jama’a Sun Girgiza

Bidiyon Yadda Wani Dan Najeriya Ke Amfani da Cokali Wajen Aski, Jama’a Sun Girgiza

  • Wani bidiyo ya yi shuhura a kafar sada zumunta na yadda wani mai aski ke amfani da cokali wajen kwalkwale kan wani yaro
  • Yadda cokalin ke cire gashin kan yaron ba tare da wata matsala ba ya sanya mutane mamakin kaifin da yake dashi
  • Sai dai, wasu mutane na ganin ba gaskiya bane, sun zargi an yi amfani da na’ura ne wajen gyara bidiyon, a zahiri ba da cokali ya yi askin ba

Wani mutum ya ba da mamaki yayin da ya fito ya nuna yadda yake aski da cokali, bidiyonsa ya yadu a kafar sada zumunta ta Intagram.

A bidiyon da @jskvibes ya yada kuma ya yi shuhura, an ga mutumin na yiwa wani yaro aski da cokali cikin sauki kamar reza, lamarin da ya girgiza jama’a.

A bidiyon, mutumin ya nuna cokalinsa ga kamera, kamar dai zai tabbatarwa mutane cewa da gaske da shi zai yi askin.

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Matashi Ya Je Banki Da Ruwa a Bokiti, Ya Yi Wanka Yayin da Mutane Ke Kallonsa a Bidiyo

An yiwa yaro aski da cokali
Bidiyon Yadda Wani Dan Najeriya Ke Amfani da Cokali Wajen Aski, Jama’a Sun Girgiza | Hoto: @jskvibes
Asali: Instagram

Aski da cokali

Yayin da ya gama nunawa mutane cokalin nasa, mutumin ya zarce yiwa yaron da ke gabansa aski.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya fara yin askin a hankali, sai kawai aka ga gashin kansa na zuwa kamar an yi amfani da reza.

Mutane da yawa a kafar sada zumunta sun yi mamaki, sun nuna rashin gamsuwa da wannan tsari na aski.

Kalli bidiyon:

Martanin jama’a

Ga kadan daga abin da wasu mutane ke cewa:

@syx.lately:

"Dama an riga an aske gashin nasa kawai sun mayar da shi ta yadda idan suka saka cokalin zai fita.”

@nikamambo:

"Ban gamsu da wannan ba. Saboda a yanzu haka zan tafi na dauko cokali.”

@switching_4_lanes:

"Malam, wannan wane irin siddabaru ne nake gani?”

@leonharvey961:

"Bayan shekaru 40 zai fada ma ‘ya’yansa ‘A shekarun da nake matashi da cokali nake aski!.”

Kara karanta wannan

"Ta Yaya Aka Yi Haka?" Matashi Ya Hasko Cikin Hadadden Gidansa Na Laka, Bidiyon Ya Ba Da Mamaki

@dmgrainger3:

"Ban taba ganin irin wannan ba a baya.”

Wani mai aski da gatari

A wani labarin kuma, an ga wani matashi da ke aski da gatari a wata kasa, inda ya bayyana dalilin da yasa yake yin hakan.

A cewarsa, ya dade yana tunanin abin da zai ja hankalin kwastomominsa, amma yanzu ya gano ta aski da da gatari ne hakan zai faru.

Mutane da yawa sun bayyana martaninsu, kuma ya ce yana samun kwastomomi da ke mika kansu ya aske da gatarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel