Ana Dab Da Fara Zaɓe a Najeriya, Majalisar Ɗinkin Duniya Tace Akwai Damuwa

Ana Dab Da Fara Zaɓe a Najeriya, Majalisar Ɗinkin Duniya Tace Akwai Damuwa

  • Ana gab da babban zaɓen 2023 majalisar ɗinkin duniya ta bayyana fargabar da take da ita kan yiwuwar zaɓen
  • Majalisar ɗinkin duniya ta lisafo wasu abubuwa huɗu dake ci mata tuwo a ƙwarya kan yiwuwar zaɓe a Najeriya
  • A cewar majalisar ɗinkin ɗuniyan waɗannan abubuwan guda huɗu ka iya shafar yiwuwar gudanar da zaɓe a Najeriya

A yayin da ake kusa da fara babban zaɓen 2023 a Najeriya, ofishin majalisar ɗinkin duniya na Najeriya ya lissafo wasu damuwowi da yake da su a kan zaɓen Rahoton Premium Times.

Za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisar tarayya a ranar 25 ga watan Fabrairu, yayin da za a gudanar da zaɓen gwamnoni da na ƴan majalisar jiha a ranar 11 ga watan Maris.

Mathias
Ana Dab Da Fara Zaɓe a Najeriya, Majalisar Ɗinkin Duniya Tace Akwai Damuwa
Asali: UGC

Kodinetan UN a Najeriya, Matthias Schmale, shine ya zayyano fargabar da hukumar ke da ita akan zaɓen a yayin wata tattaunawa da Premium Times

Kara karanta wannan

Kwana 7 Gabanin Zaben 2023, Babbar Kotu Ta Kori Ɗan Takarar Jam'iyyar APC

"Muna fargabar a ɗaga zaɓuka saboda rikici," A cewar sa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ba rikicin da ake fama da shi a Arewa maso Gabas kaɗai Mr Schmale, yayi nuni da shi ba, hada rikicin da ake fama da shi a Kudu maso Gabas da wani yanki na Arewa maso Yamma.

Yace rikice-rikicen za su iya shafar gudanar da zaɓen da kuma sakamakon sa.

Wasu abubuwa guda biyu da UN ke nuna damuwar ta akai sune matsalar rashin man fetur da kuma ƙarancin kuɗi da ya addabi ko ina a Najeriya.

“Na bayyana ƙaluɓalen da za a fuskanta a wajen shirya zaɓen nan lokacin ɗauko kayan aiki da ma'aikata zuwa rumfunan zaɓe, hakan yana da alaƙa da rashin man fetur da kuma ƙarancin kuɗin da ake fama da su," Inji shi

Damuwa ta huɗu da Mr Schmale yayi magana akai itace ƙalaman tsana da ƴan siyasa ke amfani da su.

Kara karanta wannan

Karancin Kuɗi: El-Rufai Ya Bayyana Ainihin Dalilin Da Yasa Aka Sauya Takardun Kuɗi

yace jam'iyyu, ƴan siyasa da magoya bayan su, sun yi kalamai na tsana waɗanda kwata-kwata ba su dace ba.

Yayi kira da a riƙa tausasa harshe sannan a gudanar da yaƙin neman zaɓe cikin zaman lafiya da mutunta abokan adawa.

Jam'iyyar APC Ta Dakatar Da Ƴar Takarar Gwamnan Jihar Adamawa

A wani labarin na daban kuma, jam'iyyar APC ta dakatar da Aisha Binani, ƴar takarar gwamnan jihar Adamawa.

Aisha Binani itace mace ɗaya tilo dake takarar gwamna a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel