Yadda Wani Malamin Addini Da Yan Uwa 2 Suka Mutu A Rijiya Saboda Bokiti A Osun

Yadda Wani Malamin Addini Da Yan Uwa 2 Suka Mutu A Rijiya Saboda Bokiti A Osun

  • Wasu yan uwa sun gamu da ajalin su a rijiya a kokarin ciro guga daga rijiya
  • Tunda farko karamin ne yayi kokarin ciro gugan amma ya makale kafin karin mutum biyo su biyo shi
  • Tuni hukumar kashe gobara ta Jihar ta iya ciro su tare da mika gawarwakin ga iyalan mamatan

Jihar Osun - Mutane uku ne suka rasu ranar Juma'a 17 ga watan Fabrairu a cikin rijiya a wajen aikin gini a Owode da ke yankin Ede, Jihar Osun, rahoton The Punch.

Mammatan, malamin addini, Adebayo Oluwasina, mai shekaru 46; Lateef Adediran, shekaru 22; da kuma Waliu Adediran, mai shekaru 31; sun gamu da ajalinsu yayin da suke kokarin ciro wani bukiti da ya fada rijiya.

Rojiya
Yadda Yan Uwa 2 Da Wani Malamin Addini Suka Mutu A Rijiya Saboda Bokiti. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Mazaunin unguwar Alaro Onigbin ya magantu kan yadda abin ya faru

Kara karanta wannan

Yan Ta'adda Sun Kai Hari Sansanin Horaswa Ta Hukumar INEC

Wani mazaunin unguwar Alaro Onigbin da ke Owodo Ede, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce Waliu da Lateef birkiloli ne da ke wa Adebayo aiki wajen gininsa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce lokacin da suke gudanar da aiki da rana, bukitin da suke amfani don janyo ruwa a rijiya ya fada rijiyar da suke aiki da ita sai daya a ciki ya shiga don ciro wa amma ya makale.

''Karamin a ciki shine ke janyo ruwa lokacin da bukitin ya fada rijiyar. Sai yaron ya fada rijiyar don ya dauko, amma bai fito ba. Bayan wasu mintuna, yayan shi, Waliu, ya fada rijiyar don ceto shi, shima sai ya makale a ciki.
''Mai gidan da ake ma aiki, Pastor Shina, shima sai ya shiga rijiyar da nufin ya ceto mutum biyun da suka makale tun da farko, amma shima ya gaza fitowa.

Kara karanta wannan

Kaico: Jinkirin 'alert' yasa ikitoci sun ki kula mata mai juna biyu, sun barta ta mutu a Kano

''Lamarin ya matukar jefa mutanen unguwar jimami har aka kira jami'an hukumar kashe gobara zuwa wajen. Jami'an sun yi nasarar fito da su daga rijiyar, sai dai ba a raye ba.''

Martanin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Osun

Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta Jihar Osun, Ibrahim Adekunle, ya tabbatar da faruwar al'amarin ga jaridar Punch ranar Asabar.

Adekunle ya ce sun ciro mutum uku daga rijiya amma a mace, ya kara da cewa sun makale ne saboda iskar gas din ammonia da ke rijyar.

Ya ce:

''Suna aiki ne a gidan Adebayo (na uku da ya fada rijiyar) lokacin da gugan su ya fada rijyar. Na farko da ya shiga ya shiga ne da nufin ciro gugan, amma sai iskar ammonia ta shake shi a cikin rijiyar.
''yayan shi, Adediran Waliyu, a kokarin ceto dan uwansa, shima ya makale. Mai gidan shima ya gwada sa'ar sa don ciro su kafin shima ya makale. A daidai lokacin ne aka sanar da hukumar kashe gobara.

Kara karanta wannan

Karancin Kudi: Gwamna Ya Samar Da Bas Din Kyauta Don Ragewa Al'ummarsa Radadin Halin Da Ake Ciki

''Mun dauki mataki a take kuma muka ciro duka mutane ukun da hadin gwiwar jami'an hukumar na jiha da gwamnatin tarayya, ofishin yan sandan Division A, Ede, da kuma mutanen unguwa. An dauke jikin su zuwa wani asibiti ba a bayyana ba a motar daukar marasa lafiya, inda aka tabbatar da mutuwarsu kuma tuni aka dankawa iyalan su gawarwakin.''

A wani rahoton kun ji cewa wata mota dauke da fasinja 10 ta fada cikin rafi kuma dukkansu sun riga mu gidan gaskiya.

The Punch ta rahoto cewalamarin ya faru ne a babban titin Sagamu-Ijebu-Ode-Benin a Odogbolu da ke jihar Ogun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164