Mota dauke da fasinjoji ta tsinduma cikin rafi, mutum 10 sun mutu

Mota dauke da fasinjoji ta tsinduma cikin rafi, mutum 10 sun mutu

- Wata mota dauke da fasinjoji a kalla guda 10 ta wuntsula cikin rafi wadda hakan ya yii sanadiyar asarar rayyyuka

- Lamarin ya faru ne a babban titin Sagamu-Ijebu-Ode-Benin a karamar hukumar Odogbolu na jihar Ogun

- Jami'an hukumar kiyaye haddura na kasa (FRSC) sun ce tayar motar da ta fashe yayin da direban ke kokarin yin overtaking hakan yasa ya wuntsula cikin rafin

A kalla fasinjoji 10 ne suka rasu a ranar Laraba yayin da wata motar haya kirar Toyota Sienna ta tsinduma cikin rafin Ososa a babban titin Sagamu-Ijebu-Ode-Benin a karamar hukumar Odogbolu na jihar Ogun.

The Punch ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne misalin karfe 4.30 na yamma kwanaki uku bayan an tsamo gawar wani ma'aikacin kwalejin Ilimi na Tai Solarin, Ijagun a Ijebu-Ode bayan motarsa ta fada cikin rafin.

Wani wanda da lamarin ya faru a gabansa ya ce motar tana kan hanyarta na zuwa Ijebu Ode bayan ta fito ne daga Sagamu.

Shaidan da ya ce baya son a bayyana sunansa a jarida ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa a kalla mutanen da ke cikin motar sun kai 10.

Ya ce motar da kwacewa direban ne bayan tayarsa ta fashe hakan yasa motar da ta fadacikin rafin.

Jami'in wayar da kan al'umma na Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa reshen Jihar Ogun, Florence Okpe ta ce, "Hatsarin ya afku ne lokacin da motar da kwacew direban motar ya yi yunkurin shiga obatekin a kan gadar amma tayarsa ta fashe wadda hakan ya sa motar ta wuntsula cikin rafin Ososa."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel