Kazamin Rikici Ya Barke Tsakanin Yan Sanda Da Matasa A Bauchi, Da Dama Sun Jikkata

Kazamin Rikici Ya Barke Tsakanin Yan Sanda Da Matasa A Bauchi, Da Dama Sun Jikkata

  • Al'umma a garin Magama-Gumau sun shiga fargaba biyo bayan rikici tsakanin jami'an yan sanda da wasu matasa
  • Gwamnatin Bauchi ta tabbatar da faruwar al'amarin tare da bada tabbacin daukar matakin da ya dace
  • Tuni dai komai ya koma daidai har gwamnati ta bada damar kowa na iya komawa harkokin kasuwancin sa

Bauchi - Wani rikici ya jikkata mutanen da ba bayyana adadin su ba biyo bayan hatsaniya tsakanin wasu matasa da jami'an yan sanda a garin Magama-Gumau da ke karamar hukumar Toro a Jihar Bauchi.

Lamarin ya auku ne bayan da tawagar yan sanda daga Abuja suka ma garin dirar mikiya don gudanar da aiki ranar Talata.

Taswirar Bauchi
Kazamin Rikici Ya Barke Tsakanin Yan Sanda Da Matasa A Bauchi, Da Dama Sun Jikkata. Hoto: Vanguard
Asali: UGC

Ganin haka ya janyo matasan garin rufe babbar hanyar Bauchi-Jos tare da kona tayoyi wanda ya jawo cinkoson ababen hawa a titin mai cike da zirga-zirga, rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Matsayar Tinubu, Atiku, Kwankwaso da Obi a kan batun Canjin N200, N500 da N1000

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mai bawa gwamna shawara kan harkokin watsa labarai na Jihar Bauchi, Mukhtar Gidado, wanda ya shaida wa yan jarida lamarin ranar Laraba, ya tabbatar da daidaituwar lamarin.

Ya ce:

''Gwamnatin Jihar Bauchi ta samu labarin rikicin da ya faru a garin Magama-Gumau da ke karamar hukumar Toro ranar Talata 14 ga Fabrairu, 2023.
''Lamarin mara dadi ya faru ne sanadiyar kame da wata tawagar yan sanda daga Abuja da ke kan aiki ta gudanar.
''Biyo bayan haka, matasa da wasu bata gari a yankin suja dauki doka a hannu ta hanyar kona taya da kuma kashe babban titi."

Ya cigaba da cewa:

''An samu shawo kan lamarin biyo bayanan da kwamishinan yan sanda ya shaidawa gwamna da kuna hadin gwiwar jami'an tsaro don kwantar da tarzoma.
''Gwamnati ta bayyana damuwar ta akan lamarin ta kuma yi kira ga mutanen yankin da su cigaba da harkokin kasuwanci tun da komai ya daidaita.''

Kara karanta wannan

Da Duminsa: DSS Ta Magantu Kan Titsiye Fani-Kayode, Tace Yanzu ta Fara

Gidado ya kuma yi gargadi cewa ''gwamnati ba zata nade hannu ta zuba ido ta bar jami'an tsaro su jawo tashin hankali a kowanne bangaren jihar ba kuma duk wanda aka kama za a yanke masa hukunci.''

Ya kuma mika sakon jajen Gwamna Bala Mohammed ga wanda suka jikkata tare da tabbatar da cewa sun hada hannu da hukumomin da ya dace don gano wanda suka aikata laifin tare da hukunta su don zama izna ga wasu.

Kotun tarayya ta rushe hukumar Ebubeagu

A baya kun ji cewa kotun tarayya da ke Abakaliki, jihar Ebonyi ta rushe hukumar tsaro ta Ebubeagu saboda zargin saba dokoki.

Kotun ta ce ta dauki matakin ne saboda korafin cin mutuncin mutane, mallakar bindiga, da kama bayin Allah ba bisa ka'ida ba da jami'an hukumar ke yin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel