Tashin Hankali Yayin da Aka Kone Bankuna Biyu a Jihar Delta, ’Yan Sanda Sun Magantu

Tashin Hankali Yayin da Aka Kone Bankuna Biyu a Jihar Delta, ’Yan Sanda Sun Magantu

  • Yayin da 'yan Najeriya ke fuskantar karancin sabbin Naira, wasu na daukar zafi da kuma yin barna a wasu jihohin
  • An kone wasu bankuna biyu a jihar Delta yayin da zaga-zanga ta barke a wata karamar hukumar jihar
  • Ya zuwa yanzu an kama mutane tara da ake zargin suna da hannu a wannan aika-aika, ana ci gaba da bincike

Jihar Delta - Rundunar ‘yan sandan jihar Delta ta bayyana cewa, akalla bankuna biyu aka kone saboda barkewar rikici yayin zanga-zangar karancin kudi a jihar.

Daily Trust ta ruwaito yadda wasu masu zanga-zanga suka mamaye tituna saboda gaza samun sabbin kudade a bankunan jihar.

Da yake martani ga faruwar lamarin, mai magana da rundunar ‘yan sandan jihar Delta, DSP Bright Edafe ya bayyana yadda lamarin ya zo da tsaiko.

An kone bankuna a Kudu
Tashin Hankali Yayin da Aka Kone Bankuna Biyu a Jihar Delta, ’Yan Sanda Sun Magantu | Hoto: David Darius
Asali: Getty Images

A cewarsa, an kama mutane tara da zargin suna hannu da kone wasu bankuna biyu na kasuwanci a karamar hukumar Udu ta jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama mutane tara, ana ci gaba da bincike

Ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter, inda ya bayyana rashin amincewar rundunar ‘yan sanda da ayyukan ta’addanci babu gaira babu dalili.

A kalamansa:

“A karamar hukumar Udu, wasu tsagerun matasa da sunan zaga-zanga sun kone bankuna biyu da ababen hawa a karamar hukumar Udu.
“Mun kama tara da muke zargi zuwa yanzu. A hakan wasu za su kira wannan abu zanga-zanga.”

'Yan Najeriya na ci gaba da zanga-zanga a yankuna daban-daban na kasar nan kan lamarin da ya shafi karancin kudi da kuma cunkoso a bankunan kasuwanci.

Tuni dai aka daina amfani da tsoffin N200, N500 da N1000 a kasar, inda aka kirkiri sabbi amma samunsu ya gagara a hannun atalakawan kasa.

Akwai kudi a CBN, bankuna sun ki zuwa dauka

A wani labarin kuma, babban bankin Najeriya (CBN) ya daura alhakin karancin sabbin Naira a hannun jama'a ga bankunan kasuwanci na kasar.

CBN ya ce, ya buga sabbin kudade wadatattu, kuma yana jiran bankuna su zo su dauka domin rabawa jama'a a kan kanta da ATM.

A jawabinsa, CBN ya ce bankunan kasuwanci sun ki zuwa domin karbar kudaden, lamarin da ya jawo tsaiko a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel