Falwaya ta rikito da Ma'aikacin NEPA yayinda yake kokarin yanke wutan unguwa

Falwaya ta rikito da Ma'aikacin NEPA yayinda yake kokarin yanke wutan unguwa

  • Ma'aikacin NEPA ya tsallake rijiya da baya yayinda ya hau falwaya yanke wuta
  • Mutan unguwa sun bayyana yadda yayi jina-jina ta baki da hanci

Ogun - Wani ma'aikatan kamfanin Ikeja Electric mai suna Tunde na kwance a asibiti sakamakon rikitowa daga kan Falwaya a Palace Way, Abule, Arepo, karamar hukumar Obafemi Owode, jihar Ogun.

Punch Metro ta tattaro cewa Tunde da abokan aikinsa sun shiga unguwar yanke wuta yayinda lamarin ya auku ranar Litnin.

A cewar rahoton, ma'aikacin ya cire wayar kenan yayinda falwayar ta rikito da shi.

Wakilin Punch ya samu labarin cewa ma'aikacin ya ji rauni sosai inda jini ya fara fitowa daga baki da hancinsa.

Wata mai idon shaida mai suna Mrs Adeosho, tace ma'aikacin da farko ya cire wata waya, amma shugabar tawagar ma'aikatan ta umurcesa ya sake hawa ya sauko da wayan.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Bincike ya nuna abinda ya kashe budurwar da aka tsinci gawarta cikin motar basarake da ya tsere

Falwaya ta rikito da Ma'aikacin NEPA yayinda yake kokarin yanke wutan unguwa
Falwaya ta rikito da Ma'aikacin NEPA yayinda yake kokarin yanke wutan unguwa

Tace:

"Ina kwance lokacin suka zo yanke mana wuta. Yayinda na fito, na ga mutumin ya hau falwaya. Sai makwabcina yana son yanke mana wuta. Abin ya tada min hankali saboda mun riga mun biya kudin wuta, amma sai aka ce kudin da muka biya yayi kadan shi yasa zasu yanke mana wuta."
"Ina cigaba da magana da makwabcina sai na ga mutumin ya sauko, amma sabuwar shugabarsu da muke ta roka ta umurcesa ya sake hawa ya sauko da wayar gaba daya."
"Kawai sai Falwayar ta fado tare da mutumin."
"Kowa ya arce da gudu saboda mun yi zaton ya mutu ne. Sai bayan mintuna goma da mutane suka taru aka ga cewa yana numfashi amma jini na zuba ta baki da hanci."

Kara karanta wannan

Son hada kan Najeriya na saka ni hauka, Okorocha ya nuna damuwarsa kan Najeriya

Mai magana da yawun kamfanin Ikeja Electric, Felix Ofulue, ya tabbatar da aukuwan hakan amma yace suna bincike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel