Jinkirin Ganin ‘Alert’ a Asibitin Kano Ya Sa Likitoci Suka Ki Kula Mata Mai Ciki, Ta Kwanta Dama

Jinkirin Ganin ‘Alert’ a Asibitin Kano Ya Sa Likitoci Suka Ki Kula Mata Mai Ciki, Ta Kwanta Dama

  • A labarin da muke samu daga Kano, an ce wata mata ta rasu bayan da asibiti suka ki kula da ita saboda jinkirin shigar kudi banki
  • Mijin matar ya bayyana yadda lamarin ya faru, amma asibitin ya ce sam abin da mijin ya fada ba gaskiya bane, ko kusa
  • A bangare guda, wasu majinyata sun tabbatar da faruwar lamarin, kana hukumomin asibitin sun fara gudanar da bincike

Jihar Kano - Wata mata mai juna biyu a Kano, Shema’u Sani Labaran ta rasa ranta a asibitin kwararru na Abdullahi Wase saboda halin ko in kula na likitoci da kuma matsalar kudi tsaba a hannu, Daily Trust ta ruwaito.

Mijin matar, Mallam Bello Fancy ya ce, mutuwarta ta faru ne saboda jinkirin shigar kudin da ya yi tiransfa daga bankinsu zuwa asusun asibitin, wanda yasa ba a saurari matarsa ba na tsawon awanni 3.

Kara karanta wannan

Matar Tinubu Ta Bayyana Babban Sirrin Farin Jinin Mijinta, Ta Ce Ba Kuɗi Bane Kamar Yadda Wasu Ke Zato

Idan baku manta ba, gwamnatin jihar Kano ta gargadi ‘yan kasuwa da masu sana’a a jihar kan daina amfani da tsoffin kudi, inda gwamna yace zai kwace lasisinsu.

Jinkirin shigar kudi ya sa aka ki kula mata mai ciki a jihar Kano
Jinkirin Ganin ‘Alert’ a Asibitin Kano Ya Sa Likitoci Suka Ki Kula Mata Mai Ciki, Ta Kwanta Dama | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

An saba umarnin Ganduje a Kano kan tsoffin kudi

Sai dai, an tattaro cewa, wasu wuraren, ciki har da ma’aikatun gwamnati sun, gidajen mai duk sun daina karbar tsoffin kudi, ciki har da asibitin da matar ta rasu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da yake zantawa da Freedom Radio, Malam Fancy ya ce, ya kai matarsa asibiti ne a lokacin da ta fara nakuda, amma aka ki karbarta saboda ya zo da tsoffin kudi kuma asibitin ba shi da POS, sai aka nemi ya yi tiransfa.

Ya ce duk da an zare kudinsa bayan tiransfa, amma asibitin ya ki kula matarsa saboda sun ce basu ga ‘alert’ na shigar kudin asusun asibitin ba, Platinum Post ta tattaro.

Kara karanta wannan

Abincin N220k: Gidan cin abincin Gusto ya fadi gaskiyar labarin 'yan mata da Abdul a Gusto

Abin da asibitin ke cewa; waye mai fadin gaskiya?

Sai dai, Daraktar asibitin, Dr. Rahila Garba ta karyata zargin da ake na cewa likitoci sun ki kula matar, inda tace hakan ba gaskiya bane.

A bangare guda, wasu majinyatan asibitin sun tabbatar da faruwar lamarin tare da cewa su ma sun gamu da tasgaron jinkirin shigar kudi asusun asibitin.

Malam Ibrahim Abdullahi, mai magana da yawun hukumar gudanarwar asibitin ya shaida cewa, sun samu labarin abin da ya faru, kuma suna ci gaba da bincike akai.

Irin wannan lamari ya faru a jihar Kaduna, inda mata mai juna biyu ta rasu saboda babu kudin da za a bayar tsaba na jinya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.