Abin Tausayi Yayin da Mata Mai Fama da Tabin Hankali Ta Jefa Jaririyarta a Masai a Jihar Kano
- Hukumar kashe gobara a jihar Kano ta bayyana yadda ta ceto wata jaririya da aka tsoma a masar a jihar
- Mahaifiyar jaririyar ce ta jefa yarinyar a masai, an ce mahaifiyar na da tabin hankali, dalilin yin haka kenan
- A wani labarin, wata budurwa ta yi tattaki a Kano domin gano inda saurayinta yake da kuma dawo dashi gida
Jihar Kano - Jami’an hukumar kashe gobara a jihar sun ceto wata jaririya da mahaifiyarsa mai tabin hankali ta jefa a masai.
An ceto jaririyar a raye jim kadan bayan da mahaifiyar mai suna Hauwa Muhammad ta jefa ta a masai, Punch ta ruwaito.

Source: UGC
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin hukumar kashe gobara ta jihar, Saminu Abdullahi ya ce:
“A ranar Laraba, 15 ga watan Faburairu, 2023, hukumar kashe gobara ta jiha ta samu kiran gaggawa da misalin karfe 10:49 na safe, daga daya daga ma’aikatanmu, Ibrahim Umar Muhammad da ya sanar da faruwar lamarin a Sabon Titi Gidan Kankara a Kano ta Tsakiya.

Kara karanta wannan
An Gano Wata Kyakkyawar Tsohuwa Mai Shekaru 150 a Najeriya, Bidiyonta Ya Ba Da Mamaki
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
“Ma’aikan kwana-kwana sun gaggauta zuwa wurin da misalin karfe 10:54 na safe inda suka tarar da mata mai shekaru 25 mai suna Hauwa Muhammad, wacce aka ce tana da tabin hankali ta jefa diyarta a masai.
“Saboda haka, ‘yan kwana-kwana da suka iso wurin sun shiga aikinsu, sun kuma yi nasarar ceto jaririyar a raye tare da mika ta ga kakanta, Abubakar Umar Usman da ke unguwar Sabon Titi.”
Abdullahi ya kara da cewa, a halin yanzu ana ci gaba da bincike kan lamarin kafin sanar da al’umma cikakken bayanin yadda abin ya faru, Pulse ta tattaro.
Hukumomin tsaro a Najeriya sun sha ceto irin wadannan yaran daga hallaka bayan samun tsaiko daga iyayensu masu tabin hankali.
Bidiyon yadda budurwa ta nemo tsohon saurayinta da ya haukace a Kano, ta gyara shi tsaf, ta mayar dashi gida
A wani labarin kuma, wata budurwa ‘yan yankin Kudancin Najeriya ta yi tattaki zuwa jihar Kano domin ganin saurayinta da ya zauce, ta dauke shi zuwa garinsu.

Kara karanta wannan
Kai Mummuna Ne: Budurwa Ta Kunyata Saurayi, Ta Ki Amincewa Ta Aure Shi, Bidiyon Ya Girgiza Intanet
A bidiyon da ta yada, ta bayyana yadda take nemansa da kuma yadda ta yi nasarar samunsa a Kano kana ta tabbatar da daukarsa zuwa asalin garinsu domin neman magani.
A cewar budurwar, saurayin nata ya kasance jami’in soja, amma wasu mutane suka yi masa tsafi ya haukace babu gaira babu dalili.
Asali: Legit.ng