Kotu Ta Rushe Hukumar Tsaro Ta Yankin Kudu Maso Gabas, Ebubeagu, Ta Bada Dalili

Kotu Ta Rushe Hukumar Tsaro Ta Yankin Kudu Maso Gabas, Ebubeagu, Ta Bada Dalili

  • Kotu ta rushe hukumar tsaro ta yankin kudu maso gabas mai suna Ebubeagu
  • Kotun ta ce ta rushe hukumar ne saboda korafin cin zarafi, kisa da mallakar bindigu
  • Gwamonin kudu maso gabas ne suka kafa Ebubeagu na nufin yaki da yan bindiga da ke adabar yankinsu

Jihar Ebonyi - Babban kotun tarayya da ke zamanta a Abakaliki, a ranar Talata 14 ga watan Fabrairu ta rushe hukumar tsaro ta kudu maso gabas, Ebubeagu a jihar Ebonyi.

A cewar kotun, ta rushe hukumar tsaron ne sakamakon take hakkin al'umma, kwace, kama mutane ba bisa ka'ida ba da amfani da bindigu, kamar yadda The Punch ta rahoto.

Ebubeagu
Kotu Ta Rushe Hukumar Tsaro Ta Yankin Kudu Maso Gabas, Ebubeagu, Ta Bada Dalili. Hoto: The Punch
Asali: Twitter

Gwamnonin yankin kudu maso gabas ne suka kafa Ebubeagu domin magance kallubalen rashin tsaro da suka hada da hare-haren yan ta'adda da ake zargin makiyaya fulani ne, wadanda suka tilastawa mutane barin gonakinsu.

Kara karanta wannan

14 Ga Watan Fabrairu: Jerin Kasashe 5 Da Basa Raya Ranar Masoya Ta Duniya

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Gwamnonin yakin kudu maso yamma sun kafa hukumae tsaro tasu mai suna Amotekun duk don kare mutanen yankinsu daga hare-haren yan bindiga kan al'ummarsu.

Amma, mazauna garin da dama sun rika kokawa cewa hukumar ta zama abin fitina gare su duk da cewa an kafa ta ne domin kare su, musamman a jihar Ebonyi da Imo inda aka kaddamar da hukumar kuma ta fi aiki.

Dalilin da yasa kotun tarayya ta soke hukumar Ebubeagu

An sha samun rahoton cin mutuncin al'umma, musamman kisar mutanen gari ba bisa alkalin doka ba da aka danganta da Ebubeagu a Imo da Ebonyi.

Biyo bayan wannan korafe-korafen cin zali da kisa ne kotun tarayya na Abakaliki a ranar Talata ta rushe hukumar.

Ta ce dalilin rushe hukumar shine keta hakkin biladama, kama mutane ba bisa ka'ida ba da mallakar bindigu.

Kara karanta wannan

Sai Kin Biyani N10m Zan Sake Ki: Wani Ango a Kano Ya Bukaci Sabuwar Amarya Mai Neman Saki

Duk da cewa doka ce ta kafa hukumar, ba a san yadda hukuncin za ta tsaya ba a yayin da ake fama da kallubalen tsaro a kasar tare da karancin jami'an tsaro da wasunsu ake zargin ba su samu horaswa da ya dace ba.

Bugu da kari, Najeriya tana aiki da tsarin tarayya na gwamnati inda jihohi ke tarayya, inda rundunar yan sandan ke da rassa a kowane jiha.

Yan bindiga sun kashe sojoji 4 a wani gari a Delta

A wani rahoton, wasu da ake zargin yan bindiga ne sun halaka jami'an sojoji hudu a karamar hukumar Ndokwa ta Yamma a jihar Delta.

Lamarin ya faru ne sakamakon harin kwanton bauna da suka kai musu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel