Gwamnatin Tarayya da CBN Zasu Yi Nazari Kan Halascin Tsoffin Naira Gobe

Gwamnatin Tarayya da CBN Zasu Yi Nazari Kan Halascin Tsoffin Naira Gobe

  • FG da babban bankin Najeriya (CBN) zasu sake nazari kan yuwuwar ƙara wa'adin tsoffin takardun naira
  • Mallam Garba Shehu ya ce har yanzun ba'a karkare ƙarar da wasu gwamnoni a Najeriya suka kai Kotun koli ba kan batun
  • Gwamnan CBN, Godwin Emefiele, ya ce yana tunanin babu bukatar ƙara wa'adi saboda yanayin ya fara sauki

Abuja - Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa zata ɗauki matakin ƙarshe kan halascin ci gaba da amfani tsoffin takardun N200, N500 da N1000 bayan Kotun koli ta gama sauraron shari'ar dake gabanta.

Jihohin Najeriya uku, Kogi, Kaduna da Zamfara sun kai ƙarar FG gaban Kotun Koli, inda suka nemi ta umarci CBN ya tsawaita wa'adin haramta tsohon naira.

Gwamnan CBN da Buhari.
Gwamnatin Tarayya da CBN Zasu Yi Nazari Kan Halascin Tsoffin Naira Gobe Hoto: CBN
Asali: Facebook

Kotun ta umarci FG da CBN su jinkirta daga haramta tsoffin naira a ranar 10 ga wata kana ta ɗage sauraron ƙarar zuwa 15 ga watan Fabrairu, 2023, a cewar rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Shin Mutane Sun Yi Asara Kenan? Matakai 3 da Zaku Bi Ku Maida Tsoffin Naira Banki Duk da Wa'adi Ya Cika

Sai dai a halin yanzun, bayanai sun nuna cewa babban bankin Najeriya CBN ya jaddada cewa ba gudu ba ja da baya game da wa'adin 10 ga watan Fabrairu.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tuni wasu 'yan Najeriya suka fara zargin gwamnatin tarayya da kuma CBN da yunkurin raina umarnin Kotu kana basu damu da ƙuncin rayuwar da mutane ke ciki ba sakamakon karancin naira.

Shin FG ta amince da ikirarin CBN?

Amma gwamnatin tarayya a daren nan, ta ce zata ɗauki matsaya ne kawai bayan Kotun koli ta gama sauraron shari'a ta yanke hukuncin ƙarshe.

Vanguard tace yayin da aka tuntuɓe shi domin ya yi tsokaci kan inda aka kwana a gwamnati, mai magana da yawun shugaban ƙasa, Mallam Garba Shehu, ya ce:

"Muna masu bayyana cewa ba gaskiya bane cewa FG ko CBN sun ɗauki matakin ƙarshe kan halasci ko haramcin tsoffin takardun naira duba da akwai shari'a kan batun a gaban Kotun Ƙoli."

Kara karanta wannan

Karin Bayani: "Tsoffin Takardun Naira Sun Daina Amfani" CBN Ya Fitar da Sabon Jawabi

"Yan Najeriya zasu ji matsayar da gwamnati tare da CBN suka ɗauka bayan Kotu ta bayyana na ta matsayar a shari'ar da za'a ci gaba da sauraro idan Allah ya kaimu gobe."

Matakai Uku Da Zaku Bi Wajen Maida Tsoffin Naira Banki Duk da Wa'adi Ya Cika

A wani labarin kuma CBN ya bayyana matakai uku da mutum zai bi idan yana son maida tsoffin takardun naira banki

Wannan na zuwa ne bayan babban bankin na kasa ya ssanar da cewa tun ranar 10 ga watan Fabrairu, 2023 tsohon N200, N500 da N1000 suka daina amfani.

Lamarin dai ya ɗaure wa mutane kai saboda Kotun koli ta dakatar da wannan wa'adin har dai an kammala shari'ar dake gabanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel