Aiwatar da Tsarin Sauya Fasalin Naira Siyasa Ce, Gwamna Wike

Aiwatar da Tsarin Sauya Fasalin Naira Siyasa Ce, Gwamna Wike

  • Gwamna Wike na jihar Ribas ya bayyana cewa tsarin sauya takardun naira ba don ci gaba aka zo da shi ba siyasa ce
  • Nyesom Wike ya ce babu wanda ke sukar tsarin a karan kansa amma hanyar aiwatar da shi ne abin dubawa
  • Haka nan gwamnan ya ce duk masu goyon bayan tsarin ba su da tausayi duba da halin ƙuncin da aka jefa talakawa

Rivers - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya sake jaddada cewa sabon tsarin da babban bankin Najeriya (CBN) ya ɓullo da shi na sauya fasalin naira siyasa ce.

Rahoton Vanguard ya tattaro cewa Wike ya bayyana cewa masu ruwa da tsakin da ke goyon bayan aiwatar da tsarin ba su da tausayi.

Gwamna Wike.
Aiwatar da Tsarin Sauya Fasalin Naira Siyasa Ce, Gwamna Wike Hoto: Wike
Asali: Facebook

Gwamnan ya yi wannan furucin ne yayin da ya karbi takardar lashe lambar yabon, "Gwarzon mutum mai dogaro da kai 2022" wanda jaridu masu zaman kansu suka ba shi a Patakwal ranar Talata.

Kara karanta wannan

Mafita Ta Samu: Mai Alfarma Sarkin Musulmi Ya Yi Magana Mai Jan Hankali Kan Sabbin Naira Na CBN

Ya ce gurbatacciyar hanyar da aka bi wurin aiwatar da tsarin sauya kuɗin ta ƙara kuntata rayuwar talakan Najeriya wanda ke fama da yanayi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Wike ya ce:

"Muna cikin matsanancin yanayi, ban damu da abinda wasu zasu ce ba, 'yan Najeriya na fama da ƙuncin rayuwa yanzu kuma a matsayin shugabanni nauyi ne a kanmu mu share hawayensu ba mu ƙara kuntata musu ba."
"Ba wanda ya ce tsarin sauya fasalin naira bai da kyau, abinda muka ce aiwatar da tsarinba zai canja komai ba, maimakon haka zai ƙara wa mutane wahalhalu musamman talaka."

Meyasa CBN ya kawo tsarin a yanzu?

Wike ya ƙara da cewa mutanen da suka matsa dole a aiwatar da tsarin saboda zai magance rashawa kuma ya hana siyan ƙuri'u a zaɓe mai zuwa, ba su da tausayi.

The Nation ta rahoto Wike na cewa:

Kara karanta wannan

Da Gaske Matasa Sun Yi Wa Gwamna Buni Ruwan Duwatsu? Gwamnatin Yobe Ta Bayyana Gaskiyar Lamari

"Gaba ɗaya tsarin ya zama siyasa kuma ba haka ya kamata ba, kai baka wadata mu da sabbin kuɗin ba amma ka ce ba zamu karbi tsofaffin ba."
"Yanzu fa kana da kuɗi mallakinka a Asusun banki amma baka da ikon zuwa ka cire dukiyarka."

Gwamnan ya ce masu cewa ya kamata 'yan Najeriya su koma tura kuɗi ta Intanet sun ji kunya saboda sun manta da yawan 'yan Najeriya musamman a karkara ba su san menene banki ba.

Shin mutane sun yi asarar tsohon kuɗin dake hannunsu kenan?

A wani labarin kuma Matakai Uku Da Zaku Bi Wajen Maida Tsoffin Naira Banki Duk da Wa'adi Ya Cika

Bayan CBN ya sanar da cewa tsoffin kuɗi sun daina aiki tun 10 ga watan nan, babban bankin ya kawo matakai uku da mutane zasu bi wajen maida sauran da suka rage hannunsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel