Ta Hadu: Bidiyon Yadda Wata Kyakkyawar Budurwa Mai Kafa Daya Ta Tika Rawa Cike Da Kwarewa Ya Ja Hankali

Ta Hadu: Bidiyon Yadda Wata Kyakkyawar Budurwa Mai Kafa Daya Ta Tika Rawa Cike Da Kwarewa Ya Ja Hankali

  • Wata kyakkyawar budurwa yar Najeriya mai kafa daya ta burge zukata soshiyal midiya da bidiyon rawanta
  • A wata wallafa da ta yi a TikTok, matashiyar ta takarar rasa cikin kwarewa kuma jama’a sun yaba kyawunta
  • Da suke martani ga bidiyon, wasu jama’a sun nuna soyayyarsu gareta sannan su yi mata addu’ar ci gaba da dawwama a farin ciki

Wata matashiyar budurwa yar Najeriya, Cindy Chilaka, ta shahara a soshiyal midiya bayan ta wallafa bidiyon rawanta a TikTok.

A bidiyon mai kayatar da zuciya, an gano matashiyar tana rawa yayin da masu amfani da soshiyal midiya ke yaba kyawunta.

Budurwa
Ta Hadu: Bidiyon Yadda Wata Kyakkyawar Budurwa Mai Kafa Daya Ta Tika Rawa Cike Da Kwarewa Ya Ja Hankali Hoto: @cindychilaka
Asali: TikTok

Sanye da jan tufafi da gajeren wando, kyakkyawar budurwar ta girgiza jikinta daidai da kidan sautin da ke tashi a bidiyon.

Jama’a da suka ci karo da bidiyon a TikTok sun yi jinjina a gareta tare da yaba karfin gwiwarta.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Roki Gwamnatin Dubai Ta Cirewa yan Najeriya Takunkumin Hana Shiga

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jama’a sun yi martani

@reshapeupyourshape ta ce:

“A zahirin Gaskiya, Allah madaukakin sarki yana da mu’ujiza. Tsayuwa a kan kafa daya kawai tare da yin rawa haka alhalin mu masu kafa biyu ba Za mu iya haka ba! Ma shaa Allah!”

@mimzytik ta ce:

“Na so karfin gwiwar ki yar’uwa. Wannan shine abun da kawai zai sa ki farin ciki kwasar nishadi ba tare da duba nakasarki ba..waw.”

@frankad18 ya rubuta:

“Ke ta daban ce. Na kasa iya tsayar da hawayena da na ga cewa kina matukar farin ciki. Ina taya ki murna yar’uwa.”

@ladyklassik ta ce:

“Kina da kyau sosai, Ina ganin ta taba haduwa da ke, mun shiga mota daya daga Ph zuwa mbaise.”

Kalli bidiyon a kasa:

Babu ni babu yiwa namiji tayin soyayya, budurwa ta bayyana yadda wani da ta so ya bada mata kasa a ido

Kara karanta wannan

Babu Kunya: Budurwa Ta Ziyarci Mahaifinta Mai Tabin Hankali a Ranar Bazdai Dinsa, Ta Yi Rawa Tare Da Shi a Bidiyo

A wani labarin, wata kyakkyawar budurwa ta bayyana yadda abubuwa suka kaya tsakaninta da wani matashi da ta hadu da shi a soshiyal midiya.

Matashiyar dai ta bibiyi shafin saurayin wanda ta ga ya yi mata sannan ta yi masa magana amma ya dungi amsa mata a dakile.

Bata yi kasa a gwiwa ba inda ta tambaye shi ko bai da budurwa amma ya ce mata yana da ita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel