'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Harin Ta'addanci Abuja, Sun Halaka Mutane 2
- 'Yan bindiga sun kai sabon hari yankin Abaji da ke birnin tarayya Abuja da daren ranar Talata 14 ga watan Fabrairu, 2023
- Wani mazaunin kauyen da abun ya faru ya ce maharan sun shigo da karfe 11:00 na dare, sun halaka mutane biyu
- Rahoto ya nuna cewa maharan sun yi awon gaba da wasu mutane da dama kuma 'yan sanda basu ce komai ba
Abuja - Wasu 'yan bindiga sun kai mummunan hari kauyen Munu dake ƙaraƙashin karamar hukumar Abaji, birnin tarayya Abuja ranar Lahadi da daddare.
Maharan sun yi ajalin mazauna ƙauyen har mutum biyu kana suka yi awon gaba da wasu da dama da ba'a san adadinsu ba zuwa yanzu.
Wani mazauni dake rayuwa a kauyen ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa 'yan bindigan sun shiga garin da misalin ƙarfe 11:00 na daren Talata.
Mutumin, wanda ya zanta da wakilin jaridar ranar Laraba da safe, ya ce 'yan ta'addan sun shiga shagon siyayya da wurin siyar da abubuwan sha sun ɗibi son ransu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yayin harin wanda ya shafe kusan awa ɗaya, majiyar ta ce:
"Wasu dakarun yan sanda da aka jibge a garin dake maƙoftaka da mu Rubochi, garin da akwai kwalejin gwamnatin tarayya, sun zo bayan mintuna 30 da tafiyar maharan."
"Sannan sun mana alkawarin zasu dawo su ci gaba da bincike kan harin don gano masu hannu."
Har zuwa yanzun jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sandan Abuja, Josephine Adeh, bata amsa kira ko sakonnin da aka tura mata ba domin jin halin da ake ciki game da harin.
Wannan ba shi ne karo na farko da 'yan bindiga suke kai hari wasu garuruwa dake karkashin babban birnin tarayya Abuja ba, a wasu lokutan har cikin birnin suna shiga, Pulse ta tattaro.
Harin 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa na daga cikin kalubalen da Najeriya ke fama da su musamman a arewaci.
Yan Bindiga Sun Harbi Shugaban PDP Na Gunduma a Jihar Imo
A wani labarin kuma Wasu tsagerun yan ta'adda sun shiga cikin gidan shugaban PDP, sun bar shi kwance a jihar Imo
Rahoto ya nuna cewa ɗan siyasan ya shiga gida da karfe 9:00 na dare ba tare da sanin yan bindiga sun masa kwantan ɓauna ba.
Wata majiya tace maharan sun harbi shugaban PDP a kafafuwansa kuma tuni aka garzaya da shi Asibitin don ba shi kulawa.
Asali: Legit.ng