Zamfara: Matawalle ya Fatattaki Dukkan NGOs Dake Fadin Jihar

Zamfara: Matawalle ya Fatattaki Dukkan NGOs Dake Fadin Jihar

  • Gwamnatin jihar Zamfara ta umarci duk wasu kungiyoyin tallafi masu zaman kansu da su gaggauta ficewa daga jihar bayan gano yadda suke cin karensu ba babbaka
  • Hakan ya zo ne bayan gano yadda kungiyar suke aiwatar da ayyukan da basu dace ba, wadanda ke janyo matsalar tsaro da munanan ayyuka
  • Haka zalika, an umarci duk wasu ma'aikatu da bangarorin gwamnati da su raba gari da NGOs din, tare da jan kunne kan hukunta duk wata ma'aikata ko bangaren gwamnati da aka kama tana alaka dasu

Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta umarci Kungiyoyin da ba na Gwamnati ba da su bar jihar bisa abun da ta siffanta da "munanan ayyuka" da suke yi.

Taswirar Zamfara
Zamfara: Matawalle ya Fatattaki Dukkan NGOs Dake Fadin Jihar. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC
"Ta kara da bayyana yadda munanan ayyukan da NGO suke bai da rijista da dokokin da ka'idojin jihar. An gano yadda wasu daga cikinsu suke assasa rashin tsaro a jihar da kewaye"

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Ya Roki Gwamnatin Dubai Ta Cirewa yan Najeriya Takunkumin Hana Shiga

Kwamishinan Tsaro da Lamurran Gida, Mamman Tsafe ya bayyana hakan a wata takarda da ta fita ranar Talata, Channels TV ta rahoto.

"Daga yanzu, Gwamnati ta umarci NGOs da ke jihar da su tattara Komar dansu su fice daga jihar da gaggawa. An umarci ma’aikata da bangarorin gwamnati da su yanke duk wata alaka da NGO, domin za a dauki tsauraran matakai da duk MDAs din da aka kama su na alaka da NGOs.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Bayan wannan sanarwan, an umarci hukumomin tsaro na jihar su sanya ido kan NGOs da ke ayyuka a jihar ba tare da yin rijistar da ta dace ba daga hukumomin da ke da alhaki ba."

Bankuna sun yi watsi da umarnin kotu, sun daina karbar tsofaffin kudi

A wani labari na daban, wasu bankunan ‘yan kasuwa a jihohin Legas, Ondo, Kwara, Kaduna da Abuja sun daina karbar tsofaffin takardun Naira.

Kara karanta wannan

Tsoffin Kudi: Gwamna Masari Ya Aika Sako Mai Muhimmanci Ga Bankuna Da Yan Kasuwa a Jihar Katsina

Kamar yadda suka bayyana, ba su jihohi suka maka a kotu ba, don haka suna jiran umarni daga babban bankin Najeriya.

Sai dai jama’a masu tarin yawa su bayyana damuwarsu kan yadda bankunan suka daina karbar tsofaffin kudin duba da sakankancewa da suka yi cewa kotun koli Najeriya tayi umarnin a cigaba da karbar tsofaffin kudin har sai an kammala shari’at.

Asali: Legit.ng

Online view pixel