Na Kasa Cire Kudina Don Siyan Magani Da Abinci: Tsoho Ya Fashe Da Kuka Wiwi a Cikin Banki

Na Kasa Cire Kudina Don Siyan Magani Da Abinci: Tsoho Ya Fashe Da Kuka Wiwi a Cikin Banki

  • Matsalar rashin Naira da ake fama da shi a kasar ya daki wani dattijho da kyau inda aka gano shi yana sharbar kuka wiwi a cikin banki saboda ya gaza karbar kudinsa
  • Yayin da yake rike da sandarsa, mutumin ya koka cewa yana matukar jin yunwa kuma yana bukatar siyan magani, ba wai bai da kudin yin hakan bane amma CBN ya yi garkuwa da shi
  • Bankuna sun rufe rassansu da dama a Najeriya saboda hare-hare daga yan Najeriya wadanda kudadensu ke hannunsu amma suka gaza karbar kudadensu saboda manufar CBN

An gano wani dattijo yana sharban kuka a cikin wani baki saboda ya gaza samun kudinsa balle ya ci abinci da siyan magani don kula da yanayin da yake ciki na rashin lafiya.

An gano dattijon, wanda ke rike da sanda a bidiyon yana kuka mai tsuma rai, yana cewa ba wai bai da kudin bane, amma ya gaza samun kudinsa a hannu don siyan magunguna kasancewar lafiyarsa na kara tabarbarewa.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Tsoho mara lafiya ya tattaro gadonsa ya dawo banki, an ki bashi kudi

Gwamnan CBN da Dattijo
Na Kasa Cire Kudina Don Siyan Magani Da Abinci: Tsoho Ya Fashe Da Kuka Wiwi a Cikin Banki Hoto: Saheed Oladele
Asali: Facebook

Yayin da yake magana cikin harshen Yarbanci, ya koka cewa ya dauki tsawon kwanaki yana jin yunwa yayin da ya dungi tsinewa babban bankin Najeriya (CBN) kan kokarin turashi kushewa alkhalin kwanansa bai kare ba.

Yan Najeriya na cikin rikici dumu-dumu na rashin wadatar takadun Naira tun bayan da babban bankin ya sanar da wa'adin daina amfani da tsoffin kudi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Koda dai wasu gwamnoni sun kalubalanci wannan mataki na gwamnatin tarayya a kotun koli kuma an yi umurnin ci gaba da amfani da tsoffi da sabbin kudin zuwa lokacin da kotu za ta yi zama a ranar Laraba, 15 ga watan Fabrairu.

Sai dai kuma, bankuna da dama sun rufe rassansu saboda hare-haren da fusatattun yan Najeriya ke kai masu saboda CBN ya gaza samar da isassun kudaden da za su gudanar da harkokinsu yayin da yan kasuwa da dama suka daina karbar tsoffin kudi.

Kara karanta wannan

Hadimin Buhari ya Bayyana Yadda ya Kwashe Mako Daya Yana Kashe N20,000, Yace Lamarin Babu Takura

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Kazeem A Badaru ya ce:

"Kuma, duk wadanda suka jefa dattawan kasarmu cikin wannan mummunan yanayi mai ban tausayi ba za su tsere ma hukuncin Allah madaukakin sarki ba."

Aideyan Erhunwmnse ya yi martani:

"Wani irin kasa ne wannan muke ciki ne wai."

Balogun Abdulbasit Umar ya ce:

"Wannan abun bakin ciki ne. Abun bakin ciki matuka. Mutanen da ke kan wannan hukunci mugwaye ne kawai."

Masari ya yi umurnin ci gaba da amfani da tsoffin kudi a jihar Katsina

A wani labarin, Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina ya umurci bankuna da yan kasuwa da su ci gaba da karbar tsoffin kudade a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel