Idan Na Sake ‘Tashin Namiji’ In Tafi a Kwance: Budurwa Tayi Nadamar Mika Kokon Soyayya Ga Saurayi

Idan Na Sake ‘Tashin Namiji’ In Tafi a Kwance: Budurwa Tayi Nadamar Mika Kokon Soyayya Ga Saurayi

  • Wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta garzaya soshiyal midiya don kokawa kan yadda wani mutum ya yi wasti da tayin soyayyar da ta yi masa
  • Da take wallafa hirarsu a soshiyal midiya, matashiyar ta sha alwashin cewa ba za ta kara furta soyayya ga da namiji ba a rayuwarta
  • Jama'a da suka karanta hirarsu sun rabu kan wanda suke goyon baya yayin da suka bayyana ra'ayoyinsu kan lamarin

Wata matashiyar budurwa yar Najeriya ta sha alwashin cewa ba za ta kara fara nuna soyayya ga namiji ba bayan yadda ta kaya tsakaninta da wani mutum.

"Idan na kara taya namiji, na tafi a tsaye," matashiyar mai suna @NanaFirdausiii, ta rubuta a shafinta na Twitter da alamar kuka yayin da ta wallafa hirarsu da mutumin mai suna Bash-Aar.

Kara karanta wannan

Budurwa ta Koka Bayan Saurayinta na Shekaru 25 yayi Aure, Ta Dauka Nauyin Karatunsa a Kasar Waje

matashi, sako da budurwa
Idan Na Sake ‘Tashin Namiji’ In Tafi a Kwance: Budurwa Tayi Nadamar Mika Kokon Soyayya Ga Saurayi Hoto: Juanmonino, Alvarez, Twitter/@NanaFirdausiii
Asali: Getty Images

Daga hirar tasu, matashiyar ta tambayi masoyin nata ko bai da budurwa, wanda ya amsa da cewar yana da ita.

Bata damu da amsar da ya bata ba inda ta sace latsa shi cewa ta duba shafinsa kuma tana sonsa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ta kara da cewar ita din kyakkyawa ce sannan ta bukaci Bash-Aar da ya bata dama a rayuwarsa. Mutumin ya dage cewa lallai shi yana soyayya da wata, amma matashiyar ta ki ja da baya.

Ta ci gaba sannan ta fada masa cewa tana da kudi amma sai ta samu amsa mara dadi.

Jama'a sun yi martani

@Aloyesamuel ya ce:

"Magana ta gaskiya, ban ga wani abun rashin da'a a cikin abun da ya fadi ba. Kawai iya gaskiyarsa ya fadi, babu shakka. Ya nuna baya ra'ayinki, a hanya mafi wahala. Ban ga wani abun rashin mutunci a martaninsa ba.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Matar Aure ta Fita da ATM din Mijinta, Tayi Waddaka da Kudinsa Son Ranta

@simified2 ta ce:

"Yanzun nan na gama bita kan yadda zan tsara wannan mutumin faaa amma da irin wannan bada kasa a idanun na hakura da kudirina."

@sumzaar ta ce:

"Gayen nan na da zafi."

@mkaeey ya ce:

"A kalla gayen na da gaskiya, kada wanda ya zo ya tsine masa cewa ya buga wasan kwallon tebur da zuciyarta."

Uwa ta yi wa diyarta baki kan ta yi aure ba tare da saninta ba

A wani labarin kuma, wata uwa ta fusata inda ta fito idon duniya don debewa diyarta albarka kan ta yi aure ba tare da saninta ba.

Ta ce da yardar Allah yarinyar za ta dandana kudarta a gidan aurenta kuma cewar ba za ta taba jin dadin mijin nata ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel