A Karo Na Uku, Gwamnan Babban Bankin Najeriya Ya Sake Ganawa da Shugaba Buhari
- Gwamnan Babban Bankin Najeriya ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin 13 ga watan Faburairu
- Ana kyautata zaton gwamnan da shugaban kasa sun tattauna ne kan batun da ya shafi sabbin Naira
- 'Yan Najeriya na ci gaba da fuskantar tashin hankali tun bayan sauya fasalin kudi da kuma daina amfani da tsoffi
Aso Rock, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi wata ganawar sirri da gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele a fadarsa ta Aso Rock da ke Abuja.
Gwamnan ya gana da Buhari a sirrance ne a karo na uku tun bayan da Najeriya ta fara fuskantar matsala kan batun sauyin kudi da karancin Naira, The Nation ta ruwaito.
Sai dai, bai yi magana da manema labarai bayan gama ganawar kana ya bar fadar Buhari.
Ya zuwa yanzu dai ba a san dalilin ganawar tasu ba, amma ana kyautata zaton ganawar na da nasaba da karancin Naira, Channels Tv ta tattaro.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Akwai kudi a CBN, bankuna sun ki dauka
Yayin da 'yan Najeriya ke ci gaba da kukan karancin sabbin Naira, CBN ya ce akwai wadatattun kudaden da ya buga, bankunan kasuwanci ne suka ki zuwa dauka.
CBN ya daura alhakin karancin Naira kan bankunan tare da hada kai da hukumar yaki da rashawa don bankado masu yiwa shirinsa zagon kasa.
An sha kama bankunan kasuwancin da suka boye sabbin kudi saboda wasu dalilai, inda suke bayyana dalilansu da wani abun daban.
Ana ci gaba da kai ruwa rana a Najeriya kan yadda sabani ke ci gaba fitowa tsakanin CBN da bankunan kasuwanci.
Kantin Abuja ya daina karbar tsoffin kudi
A wani labarin kuma, kunji yadda wani kantin siyayya ya kauracewa amfani da tsoffin kudaden kasar duk kuwa da umarnin kotun koli na ci gaba da kashe tsoffin N200, N500 da N1000.
Kantin ya bayyana cewa, bai samu wata sanarwa a hukumance da ya amince a ci gaba da tu'ammuli da kudaden da tun CBN ya ce ba za a ci gaba da amfani dasu ba.
Idan baku manta ba, CBN ya ce daga ranar 10 ga watan Faburairu za a daina amfani da tsoffin kudi, lamarin da ya kawo tsaiko.
Asali: Legit.ng