NDLEA Ta Cafke Babban Faston Coci Kan Yunkurin Safarar Miyagun Kwayoyi Zuwa Dubai Cikin Jarkokin Manja

NDLEA Ta Cafke Babban Faston Coci Kan Yunkurin Safarar Miyagun Kwayoyi Zuwa Dubai Cikin Jarkokin Manja

  • Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, ta sake sanar da samun nasarar dakile fita da miyagun kwayoyi Dubai
  • A cewar Hukumar ta NDLEA, ta kama wani malamin coci da abokan harkallarsa guda biyu
  • Ana zargin wanda aka kama da cusa tabar wiwi a cikin jarkar manja don fita da ita kasar da ke gabas ta tsakiya

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta kama wani babban malamin coci tare da abokan aikinsa biyu da ke kokarin fita da miyagun kwayoyi zuwa Dubai, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE).

Hukumar ta bayyana haka ta hannun mai magana da yawun ta, Mr Femi Babafemi, a wata sanarwa ta shafin sada zumunta da Legit.ng ta gano ranar Lahadi, 12 ga Fabrairu.

Suspects
NDLEA Ta Cafke Babban Faston Coci Kan Yunkurin Safarar Miyagun Kwayoyi Zuwa Dubai Cikin Jarkokin Manja. Hoto: @ndlea_nigeria
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Karfin hali: EFCC ta kama shugabanta na bogi, ya damfari mutane kudi masu yawa

Kamar yadda yake kunshe cikin sanarwar, malamin cocin, tare da abokan harkallarsa biyu, ya shiga hannu ne yana kokarin fitar da sinadarin methamphetamine da kuma tabar wiwi zuwa kasar da ke gabas ta tsakiya.

Sanarwar ta ce:

''Malamin coci ya shiga hannu!"

Ka tafi dakin bauta domin neman tsari amma an samu wani ya mayar da kai mai safarar kwayoyi.

''Koma ya ake ciki, za ku ji cikakken bayani game da kama wani malamin coci da abokan aikinsa da hukumar NDLEA reshen Jihar Lagos tayi a kokarin fitar da wasu miyagun kwayoyi zuwa Dubai a rahoton mu na rana.''

NDLEA ta tona asirin masu safarar miyagun kwayoyi

Kamar yadda PM News suka ruwaito, malamin cocin sunan sa Priest Nnodu Azuka Kenrick, na cocin gamayyar Seraphic da Sabbath.

Legit.ng ta ruwaito abokan nasa sune Udezuka Udoka dalibi a makarantar Emmanuel College of Theology, Samanta, Ibadan da Oyoyo Mary Obasi a matsayin mai wakilci.

Kara karanta wannan

Shin karancin Naira zai shafi zaben bana? Jami'in INEC ya yi gargadi mai daukar hankali

Bidiyoyin da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna yadda aka dura sinadarin a jarkokin manja.

NDLEA ta kama wata mata mai ciki dauke da miyagun kwayoyi a Legas

A wani rahoton kun ji cewa jami'an hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyi a Najeriya, NDLEA, ta ce ta damke wata mata mai ciki a filin jiragen sama na Murtala Mohammad a Ikeja Legas, dauke da wani abu da ake zargin miyagun kwayoyi ne.

An kama Mrs Sylvester Gloria Onome ne a ranar Litinin 30 ga watan Janairun 2023 kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel