An Kama Wanda Ya Kai Wa Tawagar Matar Gwamnan Adamawa Hari

An Kama Wanda Ya Kai Wa Tawagar Matar Gwamnan Adamawa Hari

  • Yan sanda a jihar Adamawa sun ce sun kama wani matashi mai suna Lot Bitrus kan zargin kai wa tawagar matar gwamnan Adamawa hari
  • Yan daba sun jefi ayarin motoccin Hajiya Lami Fintiri ne a ranar Asabar yayin da suke hanyar shiga kauyen Muchala don halartar taron matan darikar katolika
  • Suleiman Nguroje, mai magana da yawun yan sandan jihar Adamawa ya ce wanda ake zargin yana tsare hannunsu kuma ana zurfafa bincike

Adamawa - Rundunar yan sandan jihar Adamawa ta kama wani Lot Bitrus, dan shekara 24 da aka ce ya kai wa ayarin motoccin matar Gwamna Ahmadu Fintiri, Hajiya Lami Fintiri, hari a ranar Lahadi.

An kai wa Fintiri hari ne a garin Muchala, kusa da Mubi a yayin da yan daba suka harbi motoccin ta yayin shiga kauyen don taron mata na katolika, rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Hukumar EFCC ta kulle Sanatan APC Gidan Yari Bisa BAdakalar N805m

Adamawa Map
Yan Sanda Sun Kama Wadanda Suka Kai Wa Tawagar Matar Gwamnan Jihar Hari. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sanarwar da kakakin yan sandna jihar, Suleiman Nguroje ya fitar ta bayyana cewa tura jami'an tsaro don tarwatsa yan daban ya yi sanadin kama Bitrus.

Ya ce za a zurfafa bincike kan wanda ake zargin.

Kalamansa:

"Wanda ake zargin, Lot Bitrus, dan shekara 24, mazaunin Muchala an kama shi ne a wani wuri da ya buya a kauyen Muchalla, karamar hukumar Mubi na arewa, yana kuma tsare a yanzu."

Kwamishinan yan sandan Adamawa ya gargadi yan siyasa

Amma, kwamishinan yan sandan jihar, Sikiru Akande ya yi kira ga yan siyasa a jihar su gargadi magoya bayansu kan kai hare-hare da ba za a amince da shi a jihar ba.

Jami'an yan sanda sun cafke wani dan shekara 16 kan zarginsa da zagin gwamnan jihar Yobe

A wani rahoton kun ji cewa rundunar yan sandan jihar Yobe ta kama wani yaro dan shekara 16 da ake zargi da zagin gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni a shafin sada zumunta.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotu Ta Bada Umurnin Tsare Magoya Bayan Atiku A Gidan Yari Har Sai Bayan Zaben Shugaban Kasa

Mahaifin yaron, Garba Isa ya yi kira ga jami'an tsaro su sako yaron wanda aka kama tun ranar 11 ga watan Disamban shekarar 2022.

A cewar rahoton da Channels Television ta tattaro an cafke yaron ne a garin Nguru sannan daga baya aka mika shi hannun rundunar yan sanda a Damaturu, babban jihar Yobe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel