Matasa Sun Kwato Wani Matashi Karfi Da Yaji Hannun Yan Sanda Kan Yaga Al-Qur'ani, Sun Kasheshi

Matasa Sun Kwato Wani Matashi Karfi Da Yaji Hannun Yan Sanda Kan Yaga Al-Qur'ani, Sun Kasheshi

  • An hallaka wani dan kasar Pakistan kan zargin wulakanta Al-Qur'ani ta hanyar lika hotunan matarsa kai
  • Wasu suna zarginsa da yin sihiri kuma hakan ya sa suka zartar masa da hukunci da kansu
  • Majalisar malaman kasar Pakistan ta yi Alla-wadai da wannan abu da matasa sukayi na daukar doka a hannu

Wasu matasa sun hallaka wani matashi Musulmi a kasar Pakistan ranar Asabar bisan zargin batancin da suka yi masa na yada littafin Al-Qur'ani mai girma.

Gomman matasa sun dira ofishin yan sanda da aka tsare matashin a unguwar Nankana Sahib, yankin Punjab inda aka ajiyeshi.

Sun mamaye ofishin yan sandan kuma suka kwace matasan hannun yan sanda karfi da yaji kan suka masa ribiti har ya mutu, hukumar yan sandan ta bayyana.

Pakistan
Matasa Sun Kwato Wani Matashi Karfi Da Yaji Hannun Yan Sanda Kan Yaga Al-Qur'ani, Sun Kasheshi Hoto: @TashirAshrafi
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

An Budewa Tawagar Motocin Gwamnan Delta Wuta, An Kashe Yan Sanda 3, Gwamnan bai cikin Motar

Jami'an yan sanda sun bayyana cewa ana tuhumar matashin ne da yaga Al-Qur'ani.

Kaakin hukumar yan sanda, Waqas Khalid, ya bayyanawa AFP cewa:

"Matasan sun dira ofishin yan sanda kuma suka bugi mutumin har lahira."
"Bayan kashehi sukayi kokarin bankawa gawarsa wuta."

Khaid yace suna gudanar da bincike kan wadanda suka kai wannan hari.

Bidiyoyi a kafafen ra'ayi da sada zumunta sun nuna yadda matasa suka yiwa ofishin yan sandan zobe.

Majalisar Malaman kasar tayi Alla-wadai

Majalisar Malaman kasar Pakistan ta bayyana cewa Shari'ar Musulunci da dokokin Pakistan ba ta baiwa kowa daman daukar doka a hannu ba.

Shugaban majalisa, Hafiz Mohammad Tahir Mahmood Ashrafi, ya yi Alla-wadai da abinda wadannan matasa suka.

Ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar.

Yace:

"Kashe mutmin da ake wa zargin batanci ga Al-Qur'ani a Nankana Sahib da kona gawarsa abinda takaici ne kuma zalunci."
"Hakkin gwamnatin Punjab ne ta dau mataki ta kama wadanda suka yi hakan kuma su hukuntasu."

Kara karanta wannan

Karancin Naira: Aiki Ya Kwabe Maku, Ku Je Ku Koyi Dambe, Shehu Sani Ga Ma'aikatan Banki

"Babu kungiya, mutum, da kungiya da ke da hakkin daukar doka a hannu."

Bidiyon:

Asali: Legit.ng

Online view pixel