Yan Najeriya Ke Boye Sabbin Kudi, CBN Ta Yi sabon Bayani Kan Halin da Ake Ciki

Yan Najeriya Ke Boye Sabbin Kudi, CBN Ta Yi sabon Bayani Kan Halin da Ake Ciki

  • CBN ya bayyana cewa wasu 'yan Najeriya masu halin aje kuɗi a gida ne suka jawo karancin takardun naira
  • Rashidat Monguno, Darakta a CBN ta ce mafita ɗaya ce masu jibge kuɗi a gidaje su fito da su a ci gaba da hada-hada
  • A cewarta, CBN ya fitar da isassun kuɗade amma har yanzun ana fama da karancinsu saboda halayen wasu tsiraru

Kwara - Babban bankin Najeriya (CBN) ya alaƙanta musabbabin ƙarancin sabbin takardun naira da halin wasu 'yan Najeriya na jibge kuɗin a gidajensu.

Daraktan sashin baiwa kwastomomi kariya a CBN, Rashidat Monguno, ita ce ta faɗi haka a Kwara ranar Alhamis yayin da ta je duba yadda bankunan Microfinance ke biyayya ga tsarin.

Sabbin naira.
Yan Najeriya Ke Boye Sabbin Kudi, CBN Ta Yi sabon Bayani Kan Halin da Ake Ciki Hoto: thecable
Asali: UGC

Rahoton The Cable ya tattaro Daraktan na cewa CBN ya samar da isassun sabbin takardun naira amma jibge kuɗi a gida da mutane ke yi ya jawo halin da ake ciki a yanzu.

Kara karanta wannan

An Sami Mafita: Bayan Hukuncin Kotu, Yan Najeriya Sun Bukaci CBN Ya Musu Abu 1 Tak Kan Sabbi da Tsoffin Kuɗi

Ta ce wasu yan Najeriya sun cika bankunan kasuwanci suna neman cire sabbin takardun N200, N500 da kuma N1000. Tace:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Saboda halayyan wasu 'yan Najeriya na ɓoye tsabar kuɗi, harda waɗanda ba su bukatar tsabar kuɗin sun garzaya suna nema don su aje ba don su kashe ba."
"Ana buga takardun kuɗi don su yi yawo amma sun hana saboda a wurin CBN idan takardun kuɗi suka fita muna tsammanin wataran zasu dawo cikin bankuna, yanzu kowa yana cirowa ya aje."
"Don haka duk yawan nairorin da muka raba, idan har muka ci gaba da wannan halin ko da CBN ya cigaba da fito da kuɗi daga nan zuwa watan Disamba ba abinda zai sauya."

Menene mafita kan wannan halin ma wasu mutane?

Rashidat Monguno ta ƙara da cewa komai zai iya komawa daidai idan masu boye kuɗin suka fito dasu suna amfani da su ta yadda zasu shiga hada-hadar kuɗaɗe a hannu.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: 'Yan Bindigan da Suka Yi Garkuwa da Kwamishina Sun Turo Sako Mai Ɗaga Hankali

Haka nan ta jaddada cewa akwai isassun takardun naira da yake yawo a hannun jama'a yanzu haka.

Daily Post ta rahoto Daraktan ta ci gaba da cewa:

"Akwai naira hannun jama'a, na zo nan Kwara tsawon mako uku kenan, kullum muna fitar da kuɗade. Maganar gaskiya idan takardun na yawo yadda aka tsara babu mai ajiye su a gida, ba zamu shiga wannan matsalar ba."

Ma'aikatan bankuna sun yi barazanar daina aiki

A wani labarin kuma Kungiyar ma'aikatan banki ta yi barazanar hana mambobinta fita aiki saboda hare-haren masu zanga-zanga.

A wata sanarwa da shugaban ƙungiyar na ƙasa ya fitar ya ce ana kai wa ma'aikata hari ba tare da hukumomin tsaro sun basu kariya ba.

Ya jaddada cewa idan har suka daina fitowa wuraren aiki ba zasu janye ba har sai tsaro ya inganta kuma an dakile masu kai masu hari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel