Sauya Fasalin Naira Ya Rage Laifin Garkuwa da Mutane da Kuma Rashawa, Malami

Sauya Fasalin Naira Ya Rage Laifin Garkuwa da Mutane da Kuma Rashawa, Malami

  • A watan Diamba 2022 gwamnatin shugaba Buhari ta sanar da cewa za'a sauya fasalin takadun Naira
  • Takardun Kudin da wannan sauyi ya shafa sune N1000, N500 da N200, daga baya aka ce a cigaba da amfani da N200
  • Yan Najeriya da dama sun bayyana irin halin da suka shiga sakamakon wannan sauyi na kudi

Antoni Janar na tarayya kuma Ministan Shari'a, Abubakar Malami, yace sauya fasalin Naira da babban bankin Najeriya CBN tayi ya rage matsalar garkuwa da mutane a kasa.

Malami, a wata hira da yayi a gidan Radio Nigeria Kaduna, tace akwai alkhairai da babu wanda ke magana a kai, rahoton DailyTrust.

A cewarsa:

"Na fada muku lamarin na kotu, zamu bi umurnin kotun amma muna da hakkin yiwa kotun bayanin amfanin wannan tsari."

Kara karanta wannan

Kaico: An gurfanar da matashi a Arewa bisa zargin satar hula da kayan sakawa

"Idan kuna kallon abubuwa mara kyau da tsarin ya kawo, wajibi ku duba abubuwa masu kyau. Idan wadannan gwamnonin sun bayyanawa kotu wahala mutane ke sha, akwai matsalolin da tsarin ke gyarara"
"Na naku misalin matsakar tsaro, yayinda aka kawo tsarin nan garkuwa da mutane ya ragu. An rage rashawa, saboda haka zamu yiwa kotu bayanin abubuwan da ke da kyau da lamarin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

MAlami
Sauya Fasalin Naira Ya Rage Laifin Garkuwa da Mutane da Kuma Rashawa, Malami# Hoto: ChannelsTV
Asali: UGC

Gwamnoni 3 sun shigar da Malami kotun koli

Gwamnoni uku karkashin jagorancin gwamna Nasir El-Rufa'i na Kaduna sun bayyyana farin ciki bisa nasarar da suka samu kan karar da suka shigar Antoni Janar da Gwamnan CBN Kotu.

El-Rufa'i ya ce lallai Malami da Godwin Emefiele sun shirya wannan tuggu ne don kada jam'iyyar APC ta samu nasara a zaben shugaban kasa.

Ganduje ya sake caccakan gwamnan bankin CBN

Kara karanta wannan

"A Cigaba Da Amfani Da Tsaffin Kudi Har Karshen Shekara": Kotun Kolin Najeriya Ta Yanke Hukunci

Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da rabon tallafi ga al'ummar jihar Kano domin rage radadin azabar da karancin Naira ya ganawa al'ummar jihar.

Gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje, a ranar Litinin ya kaddamar da rabon a gidan gwamnatin jihar.

Ya bayyana cewa jiharsa ce tafi wahala da wannan tsari na sauya fasalin Naira da bankin CBN yayi.

A cewarsa:

"Bamu muka kawo wannan lamarin ba, kuma bamu yi fatan ya faru da mu ba. Babu dadi ko kadan. Mun yi rabon kayan tallafi irin wannan a lokacin COVID-19."

Asali: Legit.ng

Online view pixel