Jerin Jihohi 15 da Watakila a Soke Zaben 2023 a Cikinsa Saboda Rashin Tsaro

Jerin Jihohi 15 da Watakila a Soke Zaben 2023 a Cikinsa Saboda Rashin Tsaro

 • Idan ba a yi komai domin dakile hare-hare da ake kaiwa wasu ‘yan kasar nan kan ofishin INEC ba, akwai yiwuwar a soke zaben 2023 a wasu jihohin
 • Wasu daga jihohin sun hada da Anambra, Enugu, Imo, Osun, Akwa Ibom da Ebonyi da wasu jihohin Arewacin Najeriya da ma Kudu maso Yamma
 • A bangaren INEC, a baya ta bayyana cewa, akwai yiwuwar rashin tsaro ya shafi zaben 2023 da ke tafe nan ba da jimawa ba

Yayin da ya saura kwanaki kadan a yi zaben 2023, yana da kyau a duba ga yanayin tsaron Najeriya da kuma yadda zai iya shafar shirin da INEC ke yi na zaben.

A watan Dismban 2022, INEC ta fitar da rahoton da ke cewa, ta samu kasa da akalla lokuta 50 da aka farmaki ofisoshinta cikin shekara biyu (2021 da 2022).

Kara karanta wannan

Wani Ya Shiga Katuwar Matsala a kan Zargin ‘Danuwan Buhari da Ganin Bayan Tinubu

Abu ne a bayyane cewa, ‘yan ta’addan IPOB sun sha daukar alhakin munanan hare-hare a yankunan Kudu maso Gabashin kasar nan.

Jihohin da watakila a soke zabe bana
Jerin Jihohi 15 da Watakila a Soke Zaben 2023 a Cikinsa Saboda Rashin Tsaro | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

A bangare guda, jihohin Arewacin Najeriya da Kudu maso Yamma su ma suna fuskantar tashe-tashen hankula daga nau’ikan ‘yan ta’adda daban-daban.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Duba da bayanan da ake dasu, Legit.ng ta tattaro jerin wasu jihohi a Najeriya, inda hare-hare kan ofisoshin INEC da na ‘yan sanda suka yawaita.

Duba jerin jihohin kamar haka

 1. Anambra
 2. Imo
 3. Osun
 4. Enugu
 5. Akwa Ibom
 6. Ebonyi
 7. Kuros Riba
 8. Abia
 9. Taraba
 10. Kaduna
 11. Borno
 12. Bayelsa
 13. Ondo
 14. Legas
 15. Ogun

Yiwuwar soke zabe a jihohi da kuma matsalar da ke tattare da haka

Yana matukar muhimmanci a lura cewa, matukar hare-hare suka ci gaba da faruwa a yankunan, INEC bata da wani zabin da ya wuce soke zabe zuwa wani lokaci daban.

Kara karanta wannan

Makarantun Adamawa, Borno, da Yobe Basu da ƙwararrun Malamai – UNICEF

Babu shakka, idan aka soke zabe saboda faruwar rashin tsaro, lamarin kan shafi kokarin INEC tare da rage kwarin gwiwar ‘yan kasa kan hukumar da gwamnati wajen samar da sahihin zabe da babu murdiya a cikinsa ba.

A bangare guda, hukumar zabe ta dage cewa, bata da shirin soke zaben 2023, kuma ta shirya tsaf don tabbatar da komai ya tafi daidai.

Hukumar ta ce, zaben bana zai kankama cikin lumana kuma tana hada kai da hukumomin da suka dace don tabbatar da hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel