Makarantun Adamawa, Borno, da Yobe Basu da ƙwararrun Malamai – UNICEF

Makarantun Adamawa, Borno, da Yobe Basu da ƙwararrun Malamai – UNICEF

  • Masana a cibiyar majalisar dinkin duniya tace gaskiyar magana babu kwararrun malamai a wasu jihohin Arewa
  • Asusun lamunin UNICEF ya saki wani rahoton bincike da aka gudanar kan wasu jihohin na Arewa
  • Jihohin da binciken ya gudana kansu sun hada da jihar Adamawa, Borno da Yobe, arewa maso gabas

Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya bayyana cewa kashi 29 cikin 100 ne kawai na makarantu a jihohi uku na Borno da Adamawa da Yobe ke da kwararrun malamai da ake bukata don koyarwa.

Babban jami’ar UNICEF na ofishin Maiduguri, Phuong T. Nguyen ta bayyana haka a lokacin da take magana a yayin tattaunawa da manema labarai don kara sanar nasarorin da aka samu wajen samar da kudi don inganta ilimi cikin gaggawa a Maiduguri.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da tankar ta fadi ta fashe, hukumar ta bayyana halin da ake ciki

Nguyen, wacce ta danganta lamarin da dalilai da dama, ta ce mummunan tasirin talauci, rashin tsaro da cutar COVID-19 sun kara taimakawa wajen tabarbarewar samun ingantaccen ilimi a yankin, rahoton Leadership.

Unicef
Makarantun Adamawa, Borno, da Yobe Basu da ƙwararrun Malamai – UNICEF
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce a fadin jihohin uku da sauran su a yankin, malami daya ke karantar da dalibai 124.

“Kusan rabin dukkan makarantun na bukatar gyara. Kashi 47 cikin 100 na makarantu a Borno ne kawai ke da kujeru, jihohin Yobe (kashi 32) da Adamawa (kashi 26) kuwa sun fi karanci.
“A Adamawa, kashi 30 cikin 100 na makarantu ne ke da isassun kayan koyar da daliban. Kashi 26% a Borno da 25% a jihar Yobe. Don haka ba abin mamaki bane, a cewar Multiple Indicator Cluster Surveys (MICS 2021) kasa da rabin yara (kashi 48.6) suka kammala karatun firamare a Arewa maso Gabashin Najeriya."

Kara karanta wannan

2023: APC na kitsa yadda za su sa kiristoci su tsane ni, Atiku ya tono sirrin 'yan APC

“Kimanin yara maza da mata da matasa miliyan 1.9 da rikicin ya shafa ba sa samun ingantaccen ilimi a yankin. Wannan ya hada da kashi 56 cikin 100 na duk yaran da ba sa zuwa makaranta,”

....In ji ta.

Ta ce ta hanyar kungiyar tallafin Global Partnership for Education (GPE) Accelerated Funding (AF), an tallafawa wajen magance kalubalen rashin kwararrun malamai da ababen more rayuwa a yankin.

Tace:

“Wannan wani shiri ne na gwamnatin tarayyar Najeriya, ta hannun ma’aikatar ilimi ta tarayya, da cibiyar malamai ta kasa (NTI) da kuma hukumar rijistar malamai ta Najeriya (TRCN).
"Shirin horaswar ya tallafa wa malamai sama da 18,000 da ba su cancanta ba amma suna aiki a Arewa maso Gabashin Najeriya don yin karatu da cin jarrabawar ATRCN."
“A ranar Asabar din da ta gabata ne aka yaye wadannan malaman tare da basu lasisi a fadin jihohin Borno da Yobe da Adamawa. Hukumar ta GPE AF ce ta dauki nauyin karatun na tsawon watanni 12 tare da tallafawar UNICEF, Teaching at the Right Level (TARL) Afirka da kungiyar malamai ta Najeriya. Horon farko na irinsa wanda ya shafi tarin malamai a Najeriya,”

Asali: Legit.ng

Online view pixel