Hadarin Mota ya Rutsa ‘Dan takaran Gwamna da Shugaban Jam’iyyar APC a Titi
- Francis Nwifuru da Stantley Emegha sun gamu da hadarin mota wajen dawowa daga kamfe a Ebonyi
- ‘Dan takaran Gwamnan na APC da shugaban jam’iyya su na cikin tawagar a lokacin da abin ya faru
- An yi sa’a Francis Nwifuru da ‘yan tawagarsa ba su samu ko kwarzane a dalilin hadarin motar ba
Ebonyi - Wani rahoto mara dadi da muke samu shi ne Rt. Hon. Francis Nwifuru da Hon. Stantley Emegha sun yi hadari a mota da yamman nan.
Daily Trust ta kawo labari a ranar Juma’a cewa Rt. Hon. Francis Nwifuru mai neman zama Gwamnan jihar Ebonyi ya gamu da wani hadarin mota.
Wannan abin ya faru ne a sa'ilin da ‘dan takarar Gwamnan na Ebonyi a karkashin APC yake tare da shugaban jam’iyyan jiha, Hon. Stantley Emegha.
Wata gingimari ce ta durowa tawagar ‘yan siyasar a kusa da wata kasuwa da ake saida kaya kan titin garin Abakiliki zuwa Afikpo a jihar ta Ebonyi.
APC tayi kamfe a kauyen Gwamna
Rahoton ya ce tsautsayin ya fadawa Francis Nwifuru ne a kan hanyarsa ta dawowa daga yawon yakin neman zabe a karamar hukumar Ohaozara.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
‘Dan takaran na jam’iyyar APC ya shirya gangami a mahaifar Gwamna mai-ci, David Umahi.
Kanin Mai girma Gwamna, Hon. Austin Umahi wanda shi ne shugaban kungiyar kamfe ta Divine Mandate yana cikin wadanda aka yi hadarin da su.
Jaridar ta ce Hon. Austin Umahi ya taki sa’a domin ya kubuta ba tare da ya samu ko rauni ba.
Mun ga ayar Ubangiji - Rt. Hon. Nwifuru
Da yake bayani, ‘dan takaran wanda shi ne shugaban majalisar dokokin Ebonyi ya godewa Ubangiji da ya kubutar da rayuwar shi da ta mutanensa.
Nwifuru ya shaidawa manema labarai dazu da rana sun gamu da hadari a hanya, amma Ubangiji ya nuna masu aya, domin duk motocinsu sun kubuta.
Shugaban majalisar dokokin mai-ci yana zargin direban babban motan ya sha giya ne, amma ‘Dan takaran bai ganin cewa da gan-gan ne aka auko masu.
Dauki daya-daya zuwa PDP
Kwanan nan aka ji labari Bola Tinubu da Ovie Omo Agege sun rasa masu goyon bayan takararsu a yankin Neja-Delta a dalilin sauya-shekarsu zuwa PDP.
APC ta rasa Sunday Oyabrade, Volvo Oyayefa, Ofene Emejor. Bini Maxwell da wasu shugabannin mazabu, yanzu sun yi alkawari za su taimaki Atiku Abubakar.
Asali: Legit.ng