Tsaffin Kwamishanoni 2, Ma'ajin PDP, da Hadimai 127 Na Tambuwal Sun Koma APC a Sokoto

Tsaffin Kwamishanoni 2, Ma'ajin PDP, da Hadimai 127 Na Tambuwal Sun Koma APC a Sokoto

  • Jam'iyyar APC a jihar Sokoto ta samu gagarumin karuwar manyan mambobin PDP cikinta makon nan
  • Uwar jam'iyyar APC ta gudana da kamfen shugaban kasa ta jihar Sokoto ranar Alhamis
  • Jiga-jigan siyasa sun bayyana cewa kashi 70% na al'ummar jihar Sokoto mabiya jam'iyya APC ne

Tsaffin kwamishanonin Tambuwal biyu, ma'ajin jam'iyyar PDP a jihar Sokoto, da hamidamn gwamnan 127 sun sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar APC.

Jiga-jigan siyasan sun bayyana sauya shekarsu ne ranar Alhamis wajen taron kamfen Tinubu/Shettima a jihar Sokoto.

Yawan wadanda suka sauya shekar ya sa shugaban uwar jam'iyyar APC, Abdullahi Adamu, ya ce PDP ta mutu a jihar Sokoto, rahoton Leadership.

Shugaban kwamitin kamfen APC, Simon Lalong, ya ce yanzu babu gwamnati a jihar Sokoto.

Sokoto
Tsaffin Kwamishanoni 2, Ma'ajin PDP, da Hadimai 127 Na Tambuwal Sun Koma APC a Sokoto Hoto: APC
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

2023: Atiku Ya Shiga Sabon Rudani, Mambobin PDP 8,000 Sun Koma APC a Arewa

Shugaban uwar jam'iyyar APC, Abdullahi Adamu, ya tarbi kwamishanonin.

Daga cikin wadanda suka sauya shekar akwai:

  1. Tsohon kwamishanan kimiya da fasaha, Hajiya Kulu Haruna
  2. Tsohon kwamishanan tsaro, Kanal Garba Moyi
  3. Jarman Sokoto, Alhaji Umarun Kwabo

Jawabin Buhari a taron

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana farin cikinsa bisa soyayya da goyon bayan da al'ummar jihar Sokoto ke yi wa jam'iyyarsa ta APC.

Ya yi kira ga al'ummar jihar su zabi Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da sauran yan takarar jam'iyyar APC a zaben 2023.

Buhari yace:

"Tun daga filin jirgin sama zuwa fadar Sultan zuwa nan mutane na tsaye a rana suna daga mana hannu, Nagode mutan Sokoto
Na rako dan takara na jam'iyyar, Ahmed Bola Tinubu, zamu goyi bayanshi kuma da yardan Allah zamu samu nasara.
Wadanda basu samu damar zuwa ba su fadawa iyalansu cewa mun zabi Bola Tinubu ya zama shugaban kasar nan da yardan Allah."

Kara karanta wannan

Daga Karshe, Jam'iyyun Adawa 29 Sun Yanke Shawara, Sun Faɗi Wanda Zasu Marawa Baya Tsakanin Tinubu da Atiku

Shi kuwa tsohon gwamnan jihar, Sanata Aliyu Magatakarda Wammako, ya bayyana cewa APC za ta samun gagarumin nasara a zaben 2023.

Ya ce APC za ta kwato mulkinta da aka sace a 2019.

Jawabin Shugaba Majalisar dattawa, Ahmed Lawan

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan, ya bayyana cewa APC ce ta lashe zaben gwamnan Sokoto amma akayi musus murdiya.

Lawan ya ce hujjar haka shine irin dandazon jama'ar da ke halarce a wajen taron kamfen.

Ahmad Lawan yace duk da PDP ce ke mulki a jihar Sokoto, kashi 80% na al'ummar Sokoto yan jam'iyyar APC ne.

Ya yi kira ga al'ummar Sokoto su zabi Bola Ahmed Tinubu matsayin shugaban kasa da kuma Sanata Kashim Shettima ranar 25 ga Febrairu, 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel