Ma'aikata Sun Yi Barazanar Rufe Bankuna Kan Hare-Haren da Ake Kai Masu

Ma'aikata Sun Yi Barazanar Rufe Bankuna Kan Hare-Haren da Ake Kai Masu

  • Kungiyar ma'aikatan bankunan kasuwanci ta yi barazanar hana mambobinta fita aiki saboda yawan hare-haren da ake kai masu
  • Babban Sakataren kungiyar na kasa, Mohammed Sheikh, ya bukaci gwamnatin tarayya ta kawo karshen wahalhalun da jama'a suka shiga
  • Fusatattun mutane sun barke da zanga-zanga a jihohi da dama kan karancin sabbin takardun naira da CBN ya sauya

Abuja - Ƙungiyar ma'aikatan Banki, Inshora da ma'aikatun kudi ta ƙasa (NUBIFIE) ta yi barazanar janye aikin mambobinta a dukkan sassan ƙasar nan.

Rahoton jaridar Daily Trust ya ce ƙungiyar ta yi wannan barazana ne sakamakon hare-haren da fusatattun 'yan Najeriya ke ci gaba da kaiwa harabar bankunan kaauwanci.

Bankunan kasuwanci.
Ma'aikata Sun Yi Barazanar Rufe Bankuna Kan Hare-Haren da Ake Kai Masu Hoto: dailytrust
Asali: UGC

NUBIFIE ta ƙara da gargadin cewa idan ta ɗauki matakin janye mambobinta ba zasu dawo bakin aiki ba har sai an dakile hare-haren da ake kaiwa kuma an tabbatar da tsaro.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Wike Ya Magantu Kan Hukuncin Kotun Koli, Ya Faɗi Matakin Da Zai Dauka Kan Sabbin Kuɗi

Sakatare janar na kungiyar NUBIFIE ta ƙasa, Mohammed Sheikh, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba 8 ga watan Fabrairu, 2023, rahoton Sahara Reporters ya tabbatar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sakataren ya nuna tsantsar damuwa da takaicinsa bisa ci gaba da kaiwa ma'aikatan bankuna hari ba tare da hukumomin tsaro sun ba su tsaro ba.

Sheikh ya buƙaci gwamnatin tarayya, babban bankin Najeriya (CBN) da masu ruwa da tsaki su yi duk me yuwuwa wajen kawo karshen wahalhalun da mutane suka shiga sanadin sauya takardun naira da takaicin cire kuɗi.

Bugu da ƙari ya roki 'yan Najeriya, waɗanda har yanzu ba su samu damar zare 'yan canjinsu da suka aje a Asusun bankuna ba da su ƙara hakuri su jure wa yanayin da ake ciki.

A sanarwan, Sheikh ya ce:

Kara karanta wannan

Abubuwa Sun Ɗau Zafi, Shugaba Buhari Ya Kori Shugaban NSITF Daga Aiki Kan Abu 1 Tak

"Don haka muna kira ga babban bankin Najeriya da ya sake nazari kan tsarin cire tsabar kuɗi wanda ya gurgunta kasuwancin masu POS sama da 200,000 a sassan Najeriya."

Banki sun yu watsi da basaraken gargajiya a Ogun

A wani labarin kuma Basarake Ya Ga Abun Mamaki Yayin da Ya Je Bankin Neman Sabbin Kuɗi

Wani reshen bankin GT a Abeokuta, babbak birnin jihar Ogun ya kunyata basaraken gargajiya na yankin Ijaiye-Titun yayin da ya je cire sabon naira.

Rahotanni sun bayyana ceqa duk da maratabawar da kwanstomomin bankin suka nuna masa, ma'aikatak bankin sun watsa masa ƙasa a ido.

Asali: Legit.ng

Online view pixel