Bill Gates Ya Fada Sabuwar Soyayya, Shekaru 2 Bayan Mutuwar Aurensa

Bill Gates Ya Fada Sabuwar Soyayya, Shekaru 2 Bayan Mutuwar Aurensa

  • Sanannen mai arzikin nan na duniya, Bill Gates, ya ci kawo da soyayya bayan shekaru biyu da mutuwar aurensa
  • An tattaro cewa, ya fada kogin soyayyar tsohuwar matar mai Oracle wacce mijinta ya rasu a shekarar 2019, Mark Hurd
  • A shekarar 2021 ne aurensu da Melinda ya kare bayan kwashe shekaru 27 da aure da kuma soyayyar shekaru 7 kafin aure

Bill Gates, fitaccen biloniyan 'dan kasuwa kuma wanda suka kafa Microsoft, ya samu sabuwar masoyiya bayan ya rabu da matarsa sama da shekara daya.

Bill Gates
Billgates Ya Fada Sabuwar Soyayya, Shekaru 2 Bayan Mutuwar Aurensa. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Kamar yadda Daily Mail, fitaccen 'dan kasuwan mai shekaru 67 yanzu yana tsaka da soyayya da Paila Hurd, tsohuwar matar Mark Hurd, tsohon mamallakin Oracle wanda ya mutu a 2019.

Gates da Paula sun kasance tsofaffin masoyan wasan tennis. An gano cewa suna halartar wurin kallon wasan na tsawon shekaru.

Kara karanta wannan

Sama da Mutum 44,000 ne suka Rasu Yayin da Girgizar Kasar Turkiyya da Syria Kawo Yanzu

Su biyun an gansu a watan da ya gabata a Melbourne da Sydney, jaridar The Cable ta rahoto hakan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ba za a iya raba su ba."

- Wani abokin masoyan biyu ya sanar da hakan.

Paula mai shekaru 60 a duniya da mijinta wanda ya rasu sakamakon cutar daji, suna da yara matta biyu tare.

Matar mai takaba yanzu ta koma sana'ar tsara taro da shiryawa tare da taimakon marasa karfi.

Gates da Melinda sun sanar da rabuwar aurensu a watan Mayun 2021, shekaru 34 bayan fara zamansu tare dannan shekaru 27 bayan aurensu.

Sun yi aure a shekarar 1994 bayan kwashe shekaru 7 suna soyayya da yara uku da suka haifa. Akwai Jennifer da Phoebe sai namiji daya mai suna Rory.

"Mun hada alaka mai matukar amfani da kusan inda mu ke aiki tare. Kuma ina matukar farin cikin cewa tare muke aiki. Ina takaici kamar yadda ta ke yi."

Kara karanta wannan

Matashi Ya Harbi Saurayin Kanwarsa Bayan Ya Kama su Suna ‘Soyayyar Shan Minti’

- Yace.

A watan Nuwamba, akwai rahotanni da ke bayyana cewa, Melinda tana soyayya da Jon Du Pre, tsohon 'dan jarida da Fox News.

Abun mamaki: Matar aure ta haifa yaro namiji rike da IUD

A wani labari na daban, wata matar aure ta sanar da yadda tayi haihuwar ba-zata duk da IUD da ta saka.

Ta sanar da cewa sun yi aure da mijinta amma basu shirya haihuwa ba, hakan yasa ta je tayi tsarin iyali amma duk da hakan sai ga ciki ta samu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel