Ya Yi Kama Da Kabari: Fasihin Matashi Ya Kera Gado Da Bulo, Ya Daura Katifa a Kai, Hotunan Ya Ja Hankali

Ya Yi Kama Da Kabari: Fasihin Matashi Ya Kera Gado Da Bulo, Ya Daura Katifa a Kai, Hotunan Ya Ja Hankali

  • Maimakon amfani da katakai kamar yadda aka saba, wani hazikin matashi ya kera gadon kasa da bulo da siminti
  • Wasu hotuna da ke nuna yadda aka fara kera jikin gadon har zuwa karshe ya haifar da zafafan martani a soshiyal midiya
  • Yayin da abun ya birge mutane yan kadan, da dama sun lissafo hatsarin da ke tattare da wannan gado da aka kera da bulo

Hounan wani gado da aka kera da bulo ya bayyana a soshiyal midiya kuma ya sa mutane da dama yamutsa gashin baki.

Wani mutum mai suna Seleipiri Braide ya yada hotunan a shafin Rant HQ Extention a Facebook, yana mai b ayyana sakamakon a matsayin mai ban al'ajabi.

Gadon kasa da matashi
Ya Yi Kama Da Kabari: Fasihin Matashi Ya Kera Gado Da Bulo, Ya Daura Katifa a Kai, Hotunan Ya Ja Hankali Hoto:Seleipiri Braide
Asali: Facebook

Hotunan Braide ya nuno mutumin babu riga yana dasa ginin gadon bayan ya gama tsara yadda zai kasance a filin gadon.

Kara karanta wannan

Fashewar Bam A Masallaci Ya Kashe Mutum 59, Fiye Da 159 Sun Yi Munanan Rauni A Pakistan

Hazikin matashin ya fara daddaura bulon kian juna da taimakon siminti don kera jikin gadon.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hoton karshe na labarin ya nuno yadda aka daura katifa a kan jikin gadon kasan da ak yi da bulo.

Jama'a sun yi martani

Favour Natural ta ce:

"Wannan ya yi kyau amma me zai faru idan mutum ya buga kafarsa jikin gadon cikin rashin sani yana tunanin gado ne na katako."

Ikye Onyekachi ta ce:

"Wannan na da matukar hatsari da zaran matarsa ta fusata shi sannan ya fara dukanta kawai su tafi daya dakin don gudun kada ta ture shi a kasa ko shi ya ture matar yana da hatsari."

Ude's Maybellina Omoye ta ce:

"Ya yi kama da kabari..smh.."

Abuka Sambukz ya ce:

"Kada ya yi kuskuren yin tsalle a kan gadon nan saboda idan ya zame sannan ya buga kansa a jikin bulon shikenan ya tafi har abada."

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Gansamemen Saurayi Ya Shiga Tashin Hankali Yayin da Za a Masa Allura Ya Ba Da Mamaki

Ibrahim Luqman ya ce:

"Sak irin abun da nake ta tunani.
"Zan yi amfani da wannan a matsayin samfuri, sannan na nuna maku nawa daga baya.
"Amma wannan ya yi mani tudu da yawa, rabin wannan ya isa."

A wani labari na daban, wata matashiya ta ajiye tsoffin kudi yan N1000, N500 da N200 a cikin akwatinta saboda tarihi tare da nunawa yan baya masu zuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel