Bawan Allah: Bidiyon Karamin Yaro Yana Gwagwiyar Naman Kaza Kan Teburin Mai Nama Ya Ja Hankali

Bawan Allah: Bidiyon Karamin Yaro Yana Gwagwiyar Naman Kaza Kan Teburin Mai Nama Ya Ja Hankali

  • Wani karamin yaro da ya yiwa mahaifinsa rakiya zuwa shagon mai siyar da nama ya aikata abun mamaki a lokacin da suka isa wajen
  • Yayin da mai siyar da naman ya mayar da hankali wajen daure wanda mahaifinsa ya siya, sai yaron ya mayar da hankali wajen gwagwiyar naman da ke tebur
  • Ya sa hakori ya datsa daya daga cikin kajin da ke kan teburin gabansa, amma yadda ya yi abun ya haddasa cece-kuce a TikTok

Jama'a sun yi martani masu ban dariya bayan cin karo da bidiyon wani karamin yaro wanda ya yi wa mahaifinsa rakiya zuwa wani shagon siyar da nama.

Bidiyon ya nuno yaron yana gwagwiyar daya daga cikin manyan kajin da aka baje a kan teburin da ke gabansa.

Karamin yaro a gaban kaji
Bawan Allah: Bidiyon Karamin Yaro Yana Gwagwiyar Naman Kaza Kan Teburin Mai Nama Ya Ja Hankali Hoto: TikTok/@4sunshinebaby.
Asali: UGC

An gano cewa mahaifinsa ya riga da ya biya kudin naman da ya siya kuma mai naman ya mayar da hankali wajen kunshe masu su a leda.

Kara karanta wannan

Ango Ya Manta Da Amarya a Wajen Shagalin Bikinsu, Ya Mayar Da Hankali Kan Wayar Hannunsa, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

Sai dai kuma yaron ya so motsa bakinsa a shagon, don haka sai ya gwagwiyi dan tsoka sannan ya lamushe abun sa hankali kwance.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Alamu sun nuna mai naman bai san da abun da yaron ke aikatawa ba amma sarai mahaifinsa ya kalle shi cike da mamaki.

Bidiyon ya haddasa martani masu ban dariya a TikTok yayin da mutane suka bukaci mahaifin yaron da ya siya wanda dan nasa ya gwagwiya.

Wasu sun ce yaron ya yi abunsa ne da zuciya daya cike da rashin sani. @4sunshinebaby ce ta wallafa bidiyon.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Yahaya Omar Mainasara ya ce:

"Yaron bai san komai ba, tana cin abun da take so ne."

@user16394256819 ya ce:

"Mahaifin ya yi kamar babu abun da ke faruwa."

@metryne2 ta ce:

"Sabon salon fadama iyaye su siya maka abu."

Kara karanta wannan

Miliyan 1 Nake Biya Duk Shekara: Matashi Ya Baje Kolin Gidan Da Yake Haya a Lagas, Bidiyon Ya Ja Hankali

Uwa ta tsinewa diyarta saboda ta yi aure ba tare da saninta ba

A wani labari na daban, mun ji cewa wata uwa ta tsinewa diyarta ta cikinta bayan yarinyar ta amarce da sahibinta ba tare da sanar da ita ba.

Da take tsine mata a bainar jama'a, uwar ta ce za ta dandana kudarta daga ita har mijinta a gidan aurensu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel