IMF Ya Shawarci Buhari da CBN su kara wa'adin amfani da tsaffin Naira

IMF Ya Shawarci Buhari da CBN su kara wa'adin amfani da tsaffin Naira

  • Asusun ba da lamuni na duniya (IMF) ya bukaci CBN ya duba yuwuwar kara wa'adin haramta amfanin da tsohon kuɗi
  • IMF a wata sanarwa da wakilinsa a Najeriya ya fitar, ya kafa hujja da halin kakanikayin da al'umma ke ciki
  • Wannan na zuwa ne mintuna kadan bayan Kotun koli ta dakatar da CBN daga shirinsa na haramta kuɗin

Abuja - Asusun ba da lamuni na duniya 'International Monetary Fund' (IMF) ya nemi babban bankin Najeriya ya ƙara wa'adin amfani da tsoffin takardun naira da ya canja.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa IMF ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, 8 ga watan Fabrairu, 2023.

Sauya naira.
IMF Ya Shawarci Buhari da CBN su kara wa'adin amfani da tsaffin Naira Hoto: thenation
Asali: UGC

IMF ya bukaci CBN ya ɗaga wa'adin daga 10 ga watan Fabrairu, saboda ganin yadda kasuwanci da hada-hadar kuɗin hannu suka rushe sakamakon sabon tsarin.

Kara karanta wannan

Akwai Matsala: Bankuna Sun Haɗe Kai, Sun Fitar da Sabuwar Sanarwa Ana Tsaka da Rashin Sabbin Kuɗi

A sanarwan jakadan IMF a Najeriya, Ari Aisen, ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Bisa la'akari da wahalhalun da jama'a suka tsinci kansu da rushewar kasuwanci da hada-hadar kuɗi sakamakon karancin takardun naira duk da matakan da CBN ya ɗauka ya kamata CBN ya duba yuwuwar kara wa'adin."

Sanarwan wacce ta fito yau Laraba na ɗauke da sa hannun Laraba S. Bonnet, Manajar Ofishin wakilin IMF a Najeriya a madadinsa, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa hakan na zuwa ne awanni bayan Kotun Koli ta dakatar da CBN daga haramta amfani da tsaffin takardun N200, N500 da N1000 daga ranar 10 ga watan Fabrairu.

Kotun, wacce ake wa laƙabi da daga ke sai Allah ya isa ta ba da umarnin ne yayin da take yanke hukuncin cikin shari'a a ƙarar da gwamnatocin jihohi uku suka shigar gabanta.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: Wike Ya Magantu Kan Hukuncin Kotun Koli, Ya Faɗi Matakin Da Zai Dauka Kan Sabbin Kuɗi

Tun da fari, CBN ya sanya wa'adin daina amfani tsaffin takardun naira uku ranar 31 ga watan Janairu, 2023 amma sakamakon matsin lamba daga 'yan Najeriya ya ƙara kwanaki 10.

Bankuna sun yi barazanar daina aiki

A wani labarin kuma Ma'aikatan bankuna a Najeriya sun yi barazanar dakatar da ayyukansu saboda yawan kai masu hare-hare

A wata sanarwa da kungiyar ma'aikatan banki, Inshora da sauran ma'aikatun kuɗi ta ƙasa ta fitar, ta ce abun ya fara ƙamari a sassan Najeriya duk saboda ƙarancin naira.

Ƙungiyar ta yi kira ga mahukunta a Najeriya da su dauki matakin kawo karshen wahalar da jama'a ke ciki domin ta haka ne kadai hankalin kowa zai kwanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel