Hukuncin Kotun Kolin Kan Naira: Tinubu Ya Jinjinawa El-Rufa'i, Matawalle da Bello Kan Shigar Da Buhari Kotu

Hukuncin Kotun Kolin Kan Naira: Tinubu Ya Jinjinawa El-Rufa'i, Matawalle da Bello Kan Shigar Da Buhari Kotu

  • Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya bayyana farin cikinsa bisa hukuncin kotun kolin Najeriya kan tsaffin Naira
  • Tinubu ya ce gwamnatin Buhari tare da CBN sun jefa yan Najeriya cikin kunci ba gaira ba dalili
  • Ya ce akwai kasashe da dama da suka sauya fasalin kudi amma basu jefa al'ummarsu cikin kunci ba

Abuja - Mai neman kujerar shugaban kasar Najeriya karkashin jam'iyyar All Progressives Congress APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya jinjinawa gwamnonin da suka kai shugaba Buhari kotu.

Bola Tinubu a jawabin da ya fitar biyo bayan hukuncin kotun koli na ranar Laraba.

Shugaban masu magana da yawun kwamitin kamfen Tinubu, Bayo Onanuga, ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar.

BUhari
Hukuncin Kotun Kolin Kan Naira: Tinubu Ya Jinjinawa El-Rufa'i, Matawalle da Bello Kan Shigar Da Buhari Kotu

Ya ce Tinubu na tare da wadannan Gwamnoni da suka tsayawa yan Najeriya bisa tsarin zalunci da kuntatawa da bankin CBN ya jefa mutane.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotun Koli Ta Haramta Yunkurin Hana Amfani Da Tsaffin Naira

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa:

"Ina son jinjinawa gwamnoninmu musamman na jam'iyyar APC wadanda suka ceto kasarmu daga rikici da tarzoma da bankin kasa CBN ta jefa kasar nan."
"Hukuncin kotun koli ta ceto kasar nan daga rugujewa."
"Muna godiya ga Alkalan kotun koli bisa goyon bayan al'umman da aka jefa cikin kunci da azaba tun lokacin da aka sanar da wannan tsari."
"Yanzu sai gwamnatin tarayya da masu ruwa da tsaki su zauna su fitar da sabon hanyar cigaba da wannan tsari ba tare da daburta lamarin al'umma ba."
"Muna da misalin kasashen da suka sauya fasalin kudaden kasarsu da ya kamata muyi koyi da su."

Kotun Koli Ta Dakatad Da Dokar Hana Amfani Da Tsaffin Naira

A yau Laraba, kotun kolin Najeriya ta dakatad da yunkurin da gwamnatin tarayya ke yi na hana amfani d atsaffin takardun Naira fari da ranar 10 ga Febrairu, 2023.

Kara karanta wannan

Matsaloli Sun Dabaibaye Kasa: Shugaba Buhari Zai Jagoranci Zaman Majalisar Magabatan Najeriya Yau Juma'a

Kwamitin Alkalan kotun guda bakwai karkashin jagoranicin Justice John Okoro, ya dakatad da shirin bisa karar da wasu gwamnonin Arewa uku suka shigar kotun, rahoton ThisDay.

Gwamnonin sun hada da Nasir El-Rufa'i na Kaduna, Muhammad Bello Matawalle na Zamfara, da kuma Yahaya Bello na jihar Kogi.

Gwamnonin uku sun bukaci kotun ta dakatad da shirin hana amfani da tsaffin takardun Naira da gwamnatin tarayya da babban bankin tarayya CBN ke kokarin yi a ranar 10 ga Febrairu, 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel