Kasa Ta Yamutse, Shugaba Buhari Ya Kira Taron Gaggawa na Majalisar Koli a Najeriya

Kasa Ta Yamutse, Shugaba Buhari Ya Kira Taron Gaggawa na Majalisar Koli a Najeriya

  • Muhammadu Buhari ya tsaida lokacin da Majalisar Kolin Najeriya za tayi zaman gaggawa a Aso Rock
  • Shugaban kasar ya kira taro ne domin a duba batun canjin kudi, wahalar man fetur da rashin tsaro
  • A karshen zaman da za ayi a ranar Juma’a, za a cin ma matsaya a kan shirye-shiryen zabe mai zuwa

FCT, Abuja - An kira wani taron gaggawa na majalisar kolin shugabannin Najeriya wanda zai gudana a ranar Juma’a, 10 ga watan Fubrairu 2023.

Daily Trust da ta fitar da rahoto a safiyar Laraba, ta shaida cewa Muhammadu Buhari da sauran manya za su zauna ne a kan halin da kasa ta ke ciki.

Makasudin zaman shi ne rigingimun da ya barke a wasu yankuna a dalilin sauyin takardun kudi da kuma wahalar man fetur da aka ta fama da shi.

Kara karanta wannan

2023: APC na kitsa yadda za su sa kiristoci su tsane ni, Atiku ya tono sirrin 'yan APC

Zaman da za ayi a fadar shugaban kasa zai tabo sha’anin rashin tsaro da shirye-shiryen zaben 2023. Za a fara taron da karfe 10:00 na safiyar ranar.

Za a gayyaci INEC, CBN da NPF

Rahoton ya tabbatar da cewa ana sa ran Gwamnan babban banki na kasa watau Godwin Emefiele zai yi wa majalisar bayani kan tsarin canjin kudi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata majiya ta ce shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu da Sufetan ‘Yan sanda na kasa, Usman Alkali Baba za su yi magana a taron.

Aso Rock
Taron Majalisar koli Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

BBC ta ce Majalisar za ta ji inda aka dosa a kan shirye-shiryen da hukumar zabe da jami’an ‘yan sanda suke yi, ganin saura 'yan kwanaki ayi zabe.

Zaben Najeriya ya gabato

A wajen zaman ne ake sa ran gwamnatin tarayya za ta dauki muhimman matakai a kan sha’anin zabe mai zuwa da kuma canjin takardun Nairori.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Gwamnan CBN ya warware zare da abawa ga shugaban INEC kan sabbin Naira

Legit.ng Hausa ta na sane Majalisar kolin ta na da hurumin da za ta ba gwamnatin tarayya shawara wajen zartar da matakin da ya shafi Najeriya.

Majalisar na kunshe da shugaban kasa da mataimakinsa, sakataren gwamnatin tarayya, tsofaffin shugaban kasa da tsofaffin Alkalan Alkalai.

Ragowar ‘yan majalisar su ne shugabannin majalisar dattawa da wakilai, Gwamnoni da Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya.

Zargin da APC take yi

Kun samu labari Salihu Lukman yana cewa akwai wasu manya a APC da ba su gamsu da Asiwaju Bola Tinubu ya karbi shugabanci kasar nan ba.

Shugaban jam'iyyar a APC na Arewa ya ce wadannan mutane ne suka nemi a ba Godwin Emefiele, Goodluck Jonathan ko Ahmad Lawan tikitin 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng