Karancin Man Fetur Zai Kau Nan da Mako Mai Zuwa, Kyari Ya Tabbatar Wa ’Yan Najeriya

Karancin Man Fetur Zai Kau Nan da Mako Mai Zuwa, Kyari Ya Tabbatar Wa ’Yan Najeriya

  • Yayin da 'yan Najeriya ke ci gaba da layin siyan man fetur a bangarori daban-daban na kasar nan a cikin kwanakin nan
  • Babban jami'in tafiyar harkokin man fetur na NNPCL ya bayyana tabbacin abubuwa za su daidaita nan da mako guda
  • Baya ga man fetur, Buhari ya ce zai kawo karshen matsalar karancin sabbin Naira nan da kwanaki bakwai

FCT, Abuja - Babban jami'in gudanarwa na kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL), Mele Kyari ya tabbatarwa 'yan Najeriya cewa, nan da kwanaki kadan batun karancin man fetur zai kau.

Kyari ya bayyana hakan ne a cikin wani bidiyon da Channels Tv ta yada da yammacin ranar Talata, 7 ga watan Faburairu.

Ya kuma bayyana cewa, ba zai ba da tabbacin za a daina layin man fetur ba sauran gidajen mai, amma tabbas nan mako guda za a samu sauki a fannin man fetur a kasar.

Kara karanta wannan

A ina kika samo: Kowa girgiza, wata mata ta samo damin kudi, tana siyar da N50k a farashin N60k

Kyari ya ce za a kawo karshen matsalar mai
Karancin Man Fetur Zai Kau Nan da Mako Mai Zuwa, Kyari Ya Tabbatar Wa ’Yan Najeriya | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"A yanzu cikin mako mai zuwa, ba ina cewa za a daina layin man a mako mai zuwa ba, a'a, saboda wasu abubuwan da sun fi karfinmu, kuma tabbas halin kasuwa zai sauya wasu lamurran.
"Amma na yi imanin cewa zamu ga sauki idan aka kwatnta da yau a cikin mako daya mai zuwa.
"Ina ba da hakuri game da lamarin a madadinmu gaba daya a masana'antar mai da gas."

Mai da sabbin Naira na ba 'yan Najeriya ciwon kai

An tattaro cewa, matsalar karancin man fetur da ta sabbin Naira na daya daga cikin abubuwan da ke ba 'yan Najeriya ciwon kai a wadannan kwanakin.

Karancin kudi da mai ya jefa 'yan Najeriya cikin cakwalkwalin rikicin tattalin arziki a bangarori daban-daban na kasar.

A wasu yankuna daban-daban, an ga faruwar zanga-zanga daga 'yan Najeriya da ke bukatar sauyin rayuwar da aka jefa su kwanan nan.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Zanga-Zanga Ya Barke a Abeokuta kan karancin Naira da tsadar mai, an kai hari Banki

Idan baku manta ba, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da tabbacin kawo karshen matsalar karancin Naira nan da kwanaki bakwai masu zuwa.

A bangare guda, wani sanata ya ce, kamata ya yi shugaban ya tabbatar da kawo karshen lamarin cikin kasa da kwanaki bakwai da ya deba ma kansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel