Godwin Emefiele Yaudarar Buhari Yayi, Ya Raina Masa Wayau: Adams Oshiomole

Godwin Emefiele Yaudarar Buhari Yayi, Ya Raina Masa Wayau: Adams Oshiomole

  • Adams Oshiomole ya caccaki gwamnan bankin Najeriya CBN bisa sauya fasalin takardun Naira
  • Tsohon gwamnan na jihar Edo ya ce gwamnan CBN wani kaidi ya shirya na hana yin zaben 2023
  • Ya ce Emefiele ya yaudari Buhari wacce cimma na sa manufar ta kansa

Tsohon shugaban uwar jam'iyyar Alla Progressives Congress APC, Adams Aliyu Oshiomole, ya yi magana mai tsaurin gaske kan gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Mr Godwin Emefiele.

Oshiomole ya bayyana cewa Emefiele yaudarar Shugaba Buhari yayi kan lamarin sauya fasalin Naira.

Ya bayyana hakan ne da daren Lahadi yayin hira a tashar ChannelsTV.

Oshinole
Godwin Emefiele Yaudarar Buhari Yayi, Ya Raina Masa Wayau: Adams Oshiomole
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewarsa:

"Wanna tsari rashin hankali ne, wannan gwamnan babu wani abun kirkin da yayi. Ko Atiku sai da ya nemi a kare wa'adin kudin."

Kara karanta wannan

Rikici Ya Barke a APC na Taraba, An Fitittiki Shugaban Jam'iyya

"Ba zai yiwu a rika yi mana mulkin kama-karya ba. Saboda kusanci na da Shugaban kasa albarkacin kujerar shugaban jam'iyyar da na rike, na san wayon da CBN ta yiwa Buhari saboda sun san yadda yake."
"Yayin neman umurnin (sauya faslain kudi), ina ganin CBN ya yaudari Buhari da sunan cewa za'a kauda da rashawa lokacin zabe."

Kalli bidiyon:

Asali: Legit.ng

Online view pixel