Jirgin NAF Ya Yi Saukar Gaggawa a Jihar Legas Bayan Samun Matsalar Tayoyi

Jirgin NAF Ya Yi Saukar Gaggawa a Jihar Legas Bayan Samun Matsalar Tayoyi

  • Jirgin saman sojin Najeriya ya samu tsaiko, ya yi saukar gaggawa a filin jirgin saman jiahr Legas da ke Kudu maso Yamma
  • An ruwaito cewa, an samu tsaiko ne lokacin da tayoyin jirgin suka samu matsala yayin da yake tashi a Ilorin
  • Ba a samu asarar rai ko rauni ba, amma an ba da umarnin binciko tushen aukuwar wannan hadarin

Jihar Legas - Wani jirgin rundunar sojin saman Najeriya (NAF) ya yi saukar gaggawa a ranar Litinin a filin jirgin saman Murtala Muhammad da ke Legas, TheCable ta ruwaito.

Wannan na fitowa ne daga wata sanarwar da Wapkerem Maigida, kakakin NAF ya fitar, inda yace jirgin ya samu matsala da tayoyinsa ne, wanda hakan ya tursasa masa sauka a filin na Legas.

Irin wannan sauka ta gaggawa kan faru ne yayin da jirgin ya samu tasgaro daga wasu sassan jikinsa don gujewa babbar asara ta rai da ka iya biya biyo baya, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Matashi Ya Harbi Saurayin Kanwarsa Bayan Ya Kama su Suna ‘Soyayyar Shan Minti’

Jirgi ya rasa iko, ya sauka a Legas
Jirgin NAF Ya Yi Saukar Gaggawa a Jihar Legas Bayan Samun Matsalar Tayoyi | Hoto: PIUS UTOMI EKPEI/AFP
Asali: Getty Images

Abin da rundunar sojin sama tace

A cewar sanarwar ta ranar 6 ga watan Fabrairu:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Wani jirgin saman sintiri kan ruwa na sojin saman Najeriya (NAF), Cessna Citation CJ3 da ke aikinsa a yau, 6 ga watan Fabrairun 2023 ya rasa tayoyinsa a garin tashi a Ilorin don haka dole ya yi saukar gaggawa a filin jirgin saman Murtala na kasa da kasa da ke Legas.
“Abin farin cikin, babu asarar rai ko rauni daga wadanda ke cikinsa ko da ke waje.
“Shugaban hafsun sojin sama, Air Marsheal Oladayo Amao ya umarci a tattara tawagar kwamitin bincike don gano musabbabin hadarin.
“NAF na ci gaba da neman hadin kai da goyon bayan jama’ar kasa yayin da take ci gaba da aikin kare Najeriya da ‘yan Najeriya.”

Jirgin saman ministan Ukraine ya fadi, mutane sun mutu

Kara karanta wannan

Karshen alewa: Matashi ya shiga tasku, an gano shi ke kai wa 'yan bindiga abinci a wata jihar Arewa

A wani labarin kuma, kun ji yadda wani jirgin saman da ya dauko ministan kasar Ukraine ya fadi, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane.

A rahoton da muka samo, an ce akalla mutane 16 suka mutu wasu kuma suka samu raunuka yayin da jirgin ya fadi kan wata makaranta.

Majiyoyi daga kasar sun tabbatar da faruwar lamarin, an kwashe gawargwarkin wadanda suka mutu zuwa asibiti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel