Dalilin da Ya Sa Tinubu Ke Yawan ‘Kwafsawa’ Yayin Magana Filin Kamfen, Naja’atu Mohammed

Dalilin da Ya Sa Tinubu Ke Yawan ‘Kwafsawa’ Yayin Magana Filin Kamfen, Naja’atu Mohammed

  • Tsohuwar jigon APC ta bayyana kadan daga abubuwan da ta sani game da halin da Tinubu ke ciki
  • Naja’atu ta bayyana yadda kwafsawar Tinubu ke zama abin damuwa tun bayan fitowarsa takara
  • A gefe guda, ta tabo batun Festus Kayemo, inda tace da kansa ya san Tinubu dan rashawa ne

Najeriya - A wani sabon batu, Naja’atu Muhammad ta sake ambato dalilin da yasa dan takarar shugaban kasa na APC, Bola Ahmad Tinubu ke yawan kwafsawa a magana.

Tsohuwar daraktar kamfen Tinubu da APC ta bayyana cewa, abin damuwa ne yadda Tinubu ke yawan subut da baka wajen zance duk sadda ya samu dama a filin kamfen, Punch ta ruwaito.

Da take magana a shirin Morning Show na Arise Tv a ranar Litinin 6 Faburairu, 2023, ta bayyana gaskiyar abin da ke faruwa.

Kara karanta wannan

Yadda Naja’atu ta bi Tinubu har kasar Waje Saboda Kwadayin Kujerar Kamfe Inji Minista

Dalilin yawan katobar zance ta Tinubu, cewar Naja'atu
Dalilin da Ya Sa Tinubu Ke Yawan ‘Kwafsawa’ Yayin Magana Filin Kamfen, Naja’atu Mohammed | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

A kalamanta:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

“Bidiyoyin Asiwaju sun bazu a duniya kowa na gani. Duk sadda ya ke kamfen, sai ya kwafsa. Bal ma, mutane ke lakkaba masa a kunne abin da zai fada.”

Tinubu maci amanar kujerarsa ne, kuma dan rashawa, inji Naja

Hakazalika, ta yi kaca-kaca tare da tono batun da ya shafi alakar Asiwaju da jigon APC Festus Kayemo da ke kare maganganunsa.

Ta bayyana yadda Kayemo ya kasance mai sukar Tinubu tare da tuhumarsa da cin amanar kujerarsa a shekarun baya, rahoton Vanguard.

A cewarta:

“Daya daga abubuwan da na fada game da Asiwaju shine rashawa da cin amana. Festus Kayemo ne a 1999 ya maka gwamnatin jihar Legas a kotu a kokarinta na wanke Asiwaju daga zargin cin amana. Ya je har kotun koli.
“Magana muke akan dattaku; sauyin mutane. Yana son Najeriya ta manta da dukkan abin da ya fada game da Asiwaju a wancan lokacin.

Kara karanta wannan

Assha: Naja'atu ta tono wani sirrin Aisha Buhari kan kitse-kitsen da take a fadar shugaban kasa

Aisha Buhari na cikin masu hana ruwa gudu a Villa

A wani labarin, kunji yadda Naja'atu ta tono batun abubuwan da ke faruwa a Villa, inda tace Aisha Buhari na daga cikin masu kitse-kitse a fadar Buhari.

Ta bayyana cewa, duba da abubuwan da ke faruwa, Aisha na da karfi da ikon sany abubuwa su faru a gwamnatin Manjo.

Ta kuma tuna yadda a baya Aisha ke zagin na kusa da Buhari masu hana ruwa gudu babu gaira babu dalili.

Asali: Legit.ng

Online view pixel