CBN: Mun Gano Wani Banki Sun Boye Miliyoyin Kudi na Makonni, Ana Karancin Naira

CBN: Mun Gano Wani Banki Sun Boye Miliyoyin Kudi na Makonni, Ana Karancin Naira

  • Ma’aikatan babban banki na bibiyar bankuna domin tabbatar da ana rabawa mutane sababbin kudi
  • Ana haka ne sai Mataimakin Darektan bankin CBN ya gano bankin da ya boye N6m a garin Ado Ekiti
  • Mr. Oluwole Owoeye ya ce kusan makonni biyu da suka wuce aka ba bankin kudi, amma an ki fitarwa

Ekiti - Wani banki ya samu kan shi a matsala a karshen makon nan bayan ma’aikatan babban banki na CBN sun gano ya boye sababbin kudi.

Rahoton da Vanguard ta fitar ya tabbatar da an samu Naira miliyan shida da aka boye a reshen wannan banki da ke garin Ado Ekiti a jihar Ekiti.

Mataimakin Darektan bankin CBN, Oluwole Owoeye, ya shaida cewa sun bankado wadannan sababbin kudi da aka boye ne da suke bincikensu.

Kara karanta wannan

Bankuna Na Samun N30m A Kullum?: Jami'in CBN Ya Bayyana Adadin Sabbin Naira Da Bankuna Ke Samu A Kullum

Ma’aikatan CBN su na zagayawa zuwa bankuna domin tabbatar da cewa an fitowa jama’a da sababbin kudin da babban bankin Najeriya ya buga.

Bankuna su na yi wa CBN zagon-kasa

Da yake jawabi, an rahoto Owoeye yana mai zargin bankin da boye kudin da gan-gan, yake cewa tun makonni biyu da suka wuce CBN ya ba su kudin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar Mataimakin Darektan babban bankin kasar, babu dalilin da za a ba bankin ‘yan kasuwa miliyoyi da nufin a ba jama’a, amma a boye Nairorin.

Banki
Mutane a layin ATM Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Bankin CBN yana zargin sauran bankuna da kawo masu tasgaro ta hanyar kin fito da sababbin kudi.

“Maganar da ake yi ina bankin a Ado Ekiti a kokarin da muke yi na tabbatar da cewa ana bin dokar da CBN ta gindaya.
Yanzu haka su na da Naira miliyan shida da suka karba daga hannun bankin CBN kusan makonni biyu da suka gabata.

Kara karanta wannan

Sabbin Naira: Shugaban 'yan bindiga ya ce an yi aikin banza, ya samu buhun kudi ya siya makamai

Ba su raba ko sisi daga cikin kudi ba, sun ce ba su iya saita na’urar bada kudinsu na ATM. Ban san menene dalilin haka ba.
Na fadakar da su game da ukubar haka na tarar N1m a duk rana, su na da na’urorin ATM, babu dalilin rike kudin nan.

- Oluwole Owoeye

A wani rahoto na New Telegraph, ana zargin an ci bankin tara a dalilin haka, aka bukaci a gaggauta zuba kudin a na’ura domin mutane su amfana.

Ana yakar Tinubu - Nasir El-Rufai

Ku na da labari Gwamna Nasir El-Rufai ya fara fallasa na kusa da Muhammadu Buhari da ke yakar Bola Tinubu ta hanyar fito da wasu tsare-tsare.

El-Rufai ya ce sai sun kunyata manyan 'Yan Arewa, sun tabbata Bola Tinubu ya ci zabe, sannan ya wanke Yemi Osinbajo daga zargin da ke wuyansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng