2023: CAN Ta Fitar da Sabbin Jerin Sunayen Yan Takarar Shugaban Kasa Da Ya Kamata Yan Najeriya Su Zaba

2023: CAN Ta Fitar da Sabbin Jerin Sunayen Yan Takarar Shugaban Kasa Da Ya Kamata Yan Najeriya Su Zaba

Kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN, ta bada umurni ga yan Najeriya kan yan takarar da ya kamata su zaba a zaben da ke tafe a watan Fabrairu.

Da ta ke magana ga mabiya da suka taho yin ibada a Family Worship Center, babban faston cocin, Sarah Omakwu, ta ce CAN ne ta aiko ta domin ta mika sako ga yan Najeriya.

Peter Obi, Tinubu da Atiku
2023: CAN Ta Fitar da Sabbin Jerin Sunayen Yan Takarar Shugaban Kasa Da Ya Kamata Yan Najeriya Su Zaba. Hoto: Photo: Peter Obi, PDP, APC
Asali: Facebook

Kalamanta:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Kungiyar CAN ne ta turo ni wurin ku, Kungiyar kiristocin na Najeriya kuma ta ce in fada muku wannan."

Da ta ke karanto sakon daga CAN mai taken "Babban Zaben 2023, Wa Za a Zaba?", Fasto Sarah ta sanar da mabiyan cewa kwamitin siyasa na kungiyar CAN ne ta fitar da sakon.

Kara karanta wannan

Assha: El-Rufai ya tona asirin wani gwamnan da ya samo N500m na sabbin Naira daga banki

Ta ce:

"Halaye na gari, cancanta, iyawa da tsare-tsare. Tabbas, bayan mun yi addu'a ya kamata mu iya nusar da ku (mutane)."

1. Hali

Da ta cigaba da magana, mai wa'azin ta ce CAN na tsammanin mutane su zabi wanda ke tsoron Allah kuma ya nuna gaskiya da adalci yayin da ya ke girmama doka.

Dole dan takarar ya kuma fahimci adalci da gaskiya ga kowa, ya girmama dukkan addinai da kabilai, tare da tausayi da tarbiya.

Dole shi ko ita su zama masu rayuwa mai tsafta kuma ba mamba ko alaka da kungiyar asiri ba.

Ta cigaba da cewa:

"Kada ya zama mai alaka da kwayoyi, tsafi ko tsatsaurin ra'ayi, babu alaka da Boko Haram ko wani irin kungiyar addini mai yaki.
"Wannan ne irin wanda za mu zaba, mutumin da dukkan mu za mu zaba. Wannan ne halayensa."

2. Cancanta

Dan takarar da ake tsammani wannan taron su zaba sai ya zama ya cancanta bisa makaman da ya rike a baya, isashen ilimi da zai iya kula da al'umma irin na Najeriya.

Kara karanta wannan

Kuyi Hakuri Da Wahalar Karancin Naira Kamar Yadda Kuke Hakuri Da Shan Magani Idan Baku Da Lafiya: Ministar Kudi

Dole dan takarar ya kuma iya kula da albarkatun kasa da al'umma.

3. Iya aiki

Bugu da kari, dan takarar da CAN za ta zaba dole ya kasance mai hangen nesa, ya iya isar da sakonsa ga mutane daban-daban kuma ya iya aiwatar da sauyin da ya ke son kawo wa.

Dole ya kasance mai koshin lafiya, ya kasance mai hankali da lafiyar jiki domin yin aikin.

4. Tsare-tsare

Da dukkan halayen da aka lissafa a sama, ana sa ran dan takarar da ya kamata yan Najeriya su jefa wa kuri'a zai iya tsarawa da aiwatar da manufofin da za su taimaka wa talakawan Najeriya.

Kada ku sayar da kuri'ar ku, Sakon CAN ga matasan Najeriya

A yayin da ake tunkarar babban zaben shekarar 2023, kungiyar kirista ta Najeriya, CAN, ta yi kira ga matasa kada su siyar da kuri'arsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel