Asiri Ya Tonu Yayin Da Yan Sanda Sun Kama Wasu Maza Biyu Da Makuden Jabun Takardun Naira

Asiri Ya Tonu Yayin Da Yan Sanda Sun Kama Wasu Maza Biyu Da Makuden Jabun Takardun Naira

  • Wasu mutane biyu masu matsakaitan shekaru sun shiga komar yan sanda saboda kama su da jabun kudi
  • An kama su da kudin da ya kai kimanin dubu dari da tamanin ₦180,000 na jabu
  • Rundunar tace za ta tura masu laifin zuwa kotu da zarar sun kammala bincike tare da tabbatar da cigaba da sanya ido kan makamanta laifukan

Jihar Enugu - Rundunar ýan sandan jihar Enugu tace jami'anta sun kama wasu mutane biyu da suke zargi da jabun kuɗi a ƙaramar hukumar Igbo-Eze yankin Ibagwa-Aka da ke jihar.

Daniel Ndukwe, mai magana da harshen rundunar, shi ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Juma'a, rahoton The Cable.

Wadanda ake zargi
Asiri Ya Tonu Yayin Da Yan Sanda Sun Kama Wasu Maza Biyu Da Makuden Jabun Takardun Naira. Hoto: The Cable
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kara karanta wannan

Kaico: Tashin hankali yayin da aka hallaka manoma da 'yan kasuwa a wata jihar

Ndukwe ya ce wanda ake zargi, Joseph Chinenye da Onyeka Kenneth Ezeja an kama su da jabun sababbain yan ₦1000 guda 180 "inda suke amfani da su don siyan man fetir".

Sanarwar ta ce:

"Bayan samun gamsasshen labari, jami'an ýan sanda dake aiki a ofishin Kudancin Igbo-Eze na rundunar ýan sandan Enugu, ranar 02/02/2023 da misalin 9.05 na dare, sun kama wani Joseph Chinenye mai shekaru 39 da Onyeka Kenneth Ezeja mai shekaru 29, duka maza, daga yankin Iheakpu-Awka a karamar hukumar Igbo-Eze ta Kudu da Onicha. Enugu-Ezike a karamar hukumar Igbo-Eze Arewa,"
''An kama su da mallakar jabun kuɗi da ya kai kimanin 180 na sababbin kuɗin da babban bankin kasa ya buga na takardun ₦1000, wanda ya kai kimanin dubu dari da tamanin (₦180,000)."

Ya cigaba da cewa:

"Binciken da aka gudanar na farko ya nuna, daga cikin abun da aka gano, takardun, wanda kashi uku ne, suna dauke da jerin lamba iri daya A/34:282656, A/46:578759, da kuma 8/93:852942; yayin da wanda ake zargin suka bayyana cewa sun samo jabun kuɗin ne a hannun wata mata a Benin, Jihar Edo.

Kara karanta wannan

Karshen alewa: Matashi ya shiga tasku, an gano shi ke kai wa 'yan bindiga abinci a wata jihar Arewa

"Bayan haka, sun kuma bayyana yunƙurin siyar da kuɗin ga wani mai sana'ar POS, wanda yaƙi amincewa, kafin su kai gidan mai a Ibagwa-Aka dake karamar hukumar Igbo-Eze, inda suke siyan man fetur.
"Wannan mutane biyu zamu aika su kotu idan muka kammala bincike a sashen binciken manyan laifuka na CID na jihar Enugu."

Ahmed Ammani, kwamishinan ýan sanda, ya tabbatar da yunƙurin ýan sanda wajen binkico laifuka tare da hukunta su, ciki harda almundahana ta kudi.

Ammani ya kuma yi kira ga jama'a da su ci gaba da taimakawa yunƙurin yan sanda, yayin da suke cigaba da kula wajen tantance kudin Naira, musamman sababbin.

Mai POS ya ba wani kudin bogi, ya gano bayan kwanaki

A yayin da babban bankin Najeriua CBN ya sauya sabbin kudi, bata gari kuma sun fara kirkirar na bogi.

Ali Ahmed Geidam, wani dan jarida ya bayana yadda wani mai sana'ar POS ya bashi kudin bogi.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu Ya Hargitse, Tsohon Minista Ya Fallasa Asirin Mutanen Dake Wa Atiku Aiki a Fadar Shugaban Kasa

Bankuna Na Samun N30m A Kullum?: Jami'in CBN Ya Bayyana Adadin Sabbin Naira Da Bankuna Ke Samu A Kowanne Rana

A wani rahoton, babban bankin kasa, CBN ya bayyana cewa yana baiwa kowanne reshen banki naira miliyan 1 na sababbin kudi.

Rahotanni sun bayyana cewa, adadin bazai ishi masu hulda da bankuna a jihar da ke da miliyoyin masu ajiya da ke bin dogayen layukan ATM suna jiran sabon kudi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel